Manyan shari'o'in zaɓen Najeriya mafi bazata ya zuwa yanzu

Nigerian politicians

Kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya na ci gaba da yanke hukunci a shari'o'in zaɓen 'yan majalisa da aka kai gabanta, bayan zaɓen 25 ga watan Fabrairu.

Ana dai yanke hukunce-hukuncen ne a rassan kotun na Abuja da Lagos kawai.

Kafofin labaran Najeriya sun ce umarnin mayar da shari'o'in zuwa waɗannan wurare da shugabar kotun ɗaukaka ƙara, Mai shari'a Monica Dongban-Mensem ta bayar tun da farko, ba ya rasa nasaba da ɗumbin ƙorafe-ƙorafe da adawar da jam'iyyu da 'yan takara suka yi ta nunawa.

Sun dai yi zargin cewa alƙalan kotunan ƙararrakin zaɓe da suka yi zamansu a jihohi, sun yi matuƙar karkata wani ɓangare a shari'o'in da suka gudanar.

Zuwa yanzu dai, kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da wasu hukunce-hukunce da ƙananan kotunan zaɓe suka yi, sannan sun warware wasu da dama.

Wasu hukunce-hukuncen kotun ɗaukaka ƙarar, sun zo wa mutane da dama da bazata, mamaki har ma da gigita fagen siyasa a wasu jihohi.

BBC ta yi duba kan wasu daga cikin waɗannan hukunce-hukunce:

Simon Bako Lalong

Simon Lalong

Asalin hoton, SIMON LALONG/FACEBOOK

Bayanan hoto, An bai wa Simon Lalong, ratar ƙuri'a 57,170, a sakamakon zaɓen da Inec ta sanar na 25 ga watan Fabrairu, kafin kotu ta soke sakamakon.

Abu mafi ban mamaki da kuma bijiro da ɗokin mutane, ga dukkan alamu game da nasarar tsohon gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a kotun ɗaukaka ƙara, shi ne yadda zai yi da nasarar da ya samu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A wata sanarwa da ya fitar, jim kaɗan bayan hukuncin kotun da ta yi zama a Abuja ranar Talata, Simon Lalong, ya ce ya samu labarin nasarar da kotu ta tabbatar masa ne daga ƙasar Switzerland.

Kotu ta ce shi ne halastaccen sanata mai wakiltar Filato ta Kudu, a lokacin da yake halartar babban taron ƙungiyar ƙwadago ta duniya a birnin Geneva.

Ya je taron ne a matsayin ministan ƙwadago da samar da ayyuka na Najeriya.

Ɗan takarar na jam'iyyar APC mai mulki, ya fuskanci ƙalubale daga takwaransa na jam'iyyar PDP, Napoleon Ninkap Bali ne, wanda hukumar zaɓe ta ce shi ne ya ci zaɓen 25 ga watan Fabrairu. Amma kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar Filato ta ƙwace nasarar a ranar 11 ga watan Satumba, kuma ta bai wa Simon Lalong.

Alƙalan kotun uku sun kafa hujjar cewa ƙuri'un da aka kaɗa wa ɗan takarar PDP, lalatattu ne saboda ba a tsayar da shi takara ta halastacciyar hanya ba.

Alƙalan ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Daudu Williams sun ce Simon Lalong wanda ya zo na biyu a zaɓen watan Fabrairu ne ya yi nasara, bisa hujjar cewa PDP da ɗan takararta ba su da ikon shiga zaɓen a idon doka.

PDP, in ji su, ta ƙi yin biyayya ga wani hukuncin babbar kotu, wanda ya ce sai ta gudanar da halastattun zaɓuka don fidda shugabanninta na mazaɓu da ƙananan hukumomi da kuma jihar gaba ɗaya.

Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa Simon Lalong wanda ya kammala wa'adin mulkin gwamna na biyu a Filato, ya samu ƙuri'a 91,674 ne, yayin da Napoleon Bali na PDP ya tashi da ƙuri'a 148,844, a zaɓen da suka kara.

Jazaman ne dai yanzu Simon Lalong, ya yanke shawara a kan muƙamin da zai riƙe tsakanin ministan ƙwadago ko wakilcin al'ummar Filato ta Kudu a majalisa.

Ga al'ada, 'yan majalisar da aka bai wa muƙaman minista a Najeriya sukan ajiye kujerar wakilcin da aka zaɓe su yi ta majalisa, su tafi ɓangaren zartarwa.

Mutane da yawa za su zuba ido su ga mataki na gaba da Lalong zai ɗauka, game da wannan kamon katar da ya yi.

Natasha Akpoti-Uduaghan

Senator Natasha

Asalin hoton, Natasha Akpoti- /Facebook

Bayanan hoto, Natasha Akpoti-Uduaghan ta zama mace ta hudu a zauren majalisar dattijan Najeriya, bayan rantsar da ita a matsayin sanata.

A ranar Alhamis 2 ga watan Nuwamban 2023 ne, Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya rantsar da sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan a zauren majalisar don fara aiki.

Ta shiga rukunin mata ƙalilan da ke wakiltar matan Najeriya a zauren majalisar tarayya. Ta ƙara a kan adadin mata uku, inda suka zama su huɗu kenan a majalisa ta goma.

Matakin rantsar da ita, ya zo ne kwana biyu, bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da Natasha, matsayin wadda ta ci ingantaccen zaɓe a watan Fabrairu, jim kaɗan da yin watsi da ƙarar Abubakar Ohere.

'Yar takarar ta jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Kogi, ta garzaya kotu ne bayan hukumar zaɓe ta ce, ita ce ta zo ta biyu a ƙuri'ar da aka kaɗa, inda ta samu 51,763, yayin da Ohere ya zo na ɗaya da ƙuri'a 52,132.

Abubakar Ohere, ɗan takarar jam'iyyar APC ne mai mulkin Najeriya, kuma Kogi na ƙarƙashin ikon Yahaya Bello, ɗaya daga cikin jiga-jigan gwamnoninta a ƙasar.

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar Kogi wadda Mai shari'a K. A. Orjiako ya jagoranta, ta ce an yi wa ɗan takarar APC aringizon ƙuri'u a tashoshin zaɓe tara na ƙaramar hukumar Ajaokuta.

Kuma da gangan, aka rage wa Natasha ƙuri'u a yankunan, sannan aka ƙi shigar mata da sakamakon da ta samu a tashoshin zaɓe uku.

Bayan kotun ta yi gyare-gyare ne, sai ta ayyana cewa Natasha ce ta ci zaɓe da ƙuri'a 54,074, yayin da abokin karawarta Abubakar Ohere ya samu 51,291.

Yayin hira da tashar Channels, Natasha ta ce irin neman mulki ta hanyar ko a mutu a yi rai da ta gani a Najeriya, ba siyasa ba ce.

“Ba za ka jefa mutane cikin hatsari, kuma ka yi shirin hallaka mutane, da lalata dukiyoyi da zagon ƙasa ga tsarin zaɓe, saboda kana so sai ɗan takararka ya yi nasara ba, sannan ka kira wannan abu, da kyawun dimokradiyya,” in ji ta.

Darlington Nwokocha

Darlington Nwokocha

Asalin hoton, Sen Darlington Nwokocha/Facebook

Zanga-zanga ta ɓarke ranar Litinin a Umuahia, babban birnin jihar Abia, kwana biyu bayan kotun ɗaukaka ƙara ta kori mai tsawatarwa na ɓangaren marasa rinjaye kuma sanata mai wakiltar Abia ta Tsakiyaa a Majalisar Dattijan Najeriya.

Kotun wadda ke zamanta a Lagos ta kori Sanata Darlington Nwokocha na jam'iyyar LP ne, sannan ta tabbatar da ɗan takarar PDP, Kanal Austin Akobundu (mai ritaya) a matsayin wanda ya ci zaɓen.

Magoya bayan Darlington da suka yi zanga-zanga a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Abia, sun yi watsi da hukuncin, inda suka nemi a sake duba shi.

A shafukan sada zumunta kuwa, an yi ta yaɗa rahotannin da, ga dukkan alamu ba na gaskiya ba ne, da ke iƙirarin cewa alƙalan kotun sun janye hukuncin da ya rusa zaɓen Sanata Darlington.

Abia Protests

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar daga jam'iyyar Labour sun yi ta kiraye-kiraye ga shugabanni a ƙasar, su sanya baki bayan yanke hukuncin.

Tun farko a watan Fabrairu, INEC ta ayyana ɗan takarar na jam'iyyar LP a matsayin wanda ya lashe zaɓen Abia ta Tsakiya, da yawan ƙuri'a 92,116, a kan babban abokin takararsa, Augustine Akobundu na PDP mai ƙuri'a 41,477.

Sai dai, Akobundu bai amince ba, don haka ya tafi kotu, inda ya ƙalubalanci sakamakon.

Duk da rashin nasara a kotun ƙararrakin zaɓe ta jihar Abia, Akobundu ya sake sheƙawa gaban kotun ɗaukaka ƙara.

A ranar Asabar da ta wuce ne, ta yanke hukuncin cewa shi ne halastaccen ɗan takarar da ya ci zaɓen ɗan majalisar dattijai na Abia ta Tsakiya.

Akobundu

Asalin hoton, nycewizy/X

Bayanan hoto, Kafin Austin Akobundu, tsohon ƙaramin ministan tsaro ya samu nasara a kotu, sakamako ya nuna cewa an kayar da shi da ratar ƙuri'a sama da 50,000.

Da yake jawabi yayin zanga-zangar nuna adawa da hukuncin, shugaban LP na jihar Abia, Ceekay Igara ya ce hukuncin tamkar fyaɗe ne ga dimokradiyya kuma fashi na ƙuri'un jama'a.

Ya bayyana mamaki kan hujjar da alƙalan kotun ɗaukaka ƙara da Mai shari'a Biobele A. Georgewill ke jagoranta, suka dogara da ita, wajen korar Darlington Nwokocha.

Inda ya ce shari'arsu iri ɗaya ce da ta ɗan majalisar wakilai na Isiala Ngwa ta Arewa da ta Kudu, wanda shi kuma suka tabbatar masa da nasara.

Elisha Abbo

Elisha Abbo

Asalin hoton, Elisha Abbo/Facebook

Bayanan hoto, Elisha Ishaku Abbo ya zunguro sama da kara, bayan kotu ta soke zaɓensa, abin da ya kai shi ga yin babban zargin da sai da ya komo bainar jama'a ya janye.

A ranar Litinin 16 ga watan Oktoba ne, kotun ɗaukaka ƙara da ke zama a Abuja, ta tabbatar da ɗan takarar PDP, Amos Yohanna a matsayin sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, bayan ta kori Elisha Abbo na APC.

Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a C. E. Nwosu-Iheme ta jingine hukuncin karamar kotu, wanda ya bai wa Abbo nasara, bayan tun farko a watan Fabrairu, hukumar zaɓe ta ayyana shi da cewa ya ci zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.

Reverend Amos Yohanna

Asalin hoton, Amos Yohanna/Facebook

Bayanan hoto, Da farko ƙaramar kotu ta kori ƙarar Yohanna Amos da ke ƙalubalantar nasarar da INEC ta bai wa Elisha Abbo, amma bai yi ƙasa a gwiwa ba.

Kotun ɗaukaka ƙara dai ta saurari muhawara daga kowanne ɓangare, sannan ta ce ta karɓi bahasin lauyan ɗan takarar PDP, bisa la'akari da sashe na 137 na dokar zaɓe, inda ta ce sakamakon ƙarara ya nuna cewa ba a yi biyayya da dokar zaɓe ba.

Kotun daga nan, sai ta rage ƙuri'u marasa sahihanci daga kowanne ɗan takara, inda ta gano cewa Amos Yohanna na PDP ne ya lashe zaɓe da rinjayen halastattun ƙuri'u.

Sa'o'i ƙalilan bayan sanar da sakamakon ne, sai Elisha Abbo ya yi wani taron manema labarai wanda ya zunguro sama da kara.

Matashin dattijon ya zargi shugaban majalisar dattijan Najeriya, da shirya maƙarƙashiyar da ta yi sanadin faɗuwarsa a gaban shari'a.

Ya kuma bayyana mamaki a kan yadda duk da ratar ƙuri'u sama da 11,000, da bai wa babban abokin takararsa Yohanna Amos Yohanna, amma kotu ta rushe nasararsa.

Sai dai daga baya, ya janye iƙirarin da ya yi, tare da neman afuwar Sanata Godswill Akpabio.

Simon Mwadkwon

Simon Mwadkon

Asalin hoton, SIMON MWADKON/FACEBOOK

Bayanan hoto, Simon Mwadkwon da kaɗan ya zarce wata huɗu a kan babban muƙaminsa na shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai, lokacin da kotu ta soke zaɓensa.

Shari'ar zaɓen shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattijan Najeriya, Sanata Simon Mwadkwon, na ɗaya daga cikin mafi gigitarwa ga magoya baya da kuma jam'iyyar PDP da ya yi wa takara.

Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ce ranar 22 ga watan Oktoba, ta soke nasarar ɗan majalisar dattijan na Filato ta Arewa.

A hukuncin da suka yanke na bai ɗaya, alƙalan kotun uku bisa jagorancin Mai shari'a Daudu Williams, sun ce jam'iyyarsa ta PDP, ba ta tsayar da shi takara bisa ingantacciyar hanya ba.

Don haka, suka ba da umarnin sake zaɓen ɗan majalisar dattijai na Filato ta Arewa a cikin kwana 90.

Suka ce a ganinsu PDP ba ta yi aiki da umarnin kotu wajen gudanar da zaɓen shugabannin jam'iyya a ƙananan hukumomi 12 ba.

Shugaban marasa rinjayen dai tun ranar 15 ga watan Satumba ya fitar da wata sanarwa, yana bayyana hukunce-hukuncen kotun ƙararrakin zaɓe da suka soke zaɓukan wasu ‘yan majalisar wakilai na jam'iyyarsu ta PDP daga Filato, a matsayin baƙon abu, har ma ya ce ba za su tabbata ba.

Simon Davou Mwadkwon ya ce yana da ƙwarin gwiwa kotun ɗaukaka ƙara za ta rusa hukunce-hukuncen ƙaramar kotun, sannan ta mayar da musu da kujerun 'yan majalisar waklansu saboda a cewarsa, ƙarara sun saɓa da matsayin Kotun Ƙoli.

Sai dai, wannan fata na Mista Mwadkwon bai cika ba, maimakon haka ma, tasa kujerar ma, ta kuɓuce.

Ya dai bayyana ƙwarin gwiwar cewa zai koma majalisa, amma wannan lokaci ne kaɗai zai nuna.

Gabriel Suswam

Gabriel Suswam

Asalin hoton, Simon Gabriel/Facebook

Bayanan hoto, Gabriel Suswam ya yi gwamna a jihar Binuwai tsawon shekara takwas daga 2007 zuwa 2015.

Gabriel Suswam na cikin ‘yan siyasar da suka ga ta-leƙo-ta-koma a zaɓen 2023.

Ya samu ƙwarin gwiwa dai lokacin da kotun ƙararrakin zaɓe ta jihar Binuwai ranar 8 ga watan Satumba, ta ce shi ne ya yi nasara a zaɓen sanata mai wakiltar Binuwai ta Arewa maso Gabas.

Amma alƙalan kotun ɗaukaka ƙara gaba ɗayansu suka ce hukuncin kuskure ne, inda suka jingine shi, tare da tabbatar da nasarar Emmanuel Udende na APC

Udende ya ci zaɓen watan Fabrairu ne a cewar Inec da yawan ƙuri’a 135,573, inda ya kayar da Suswam mai ƙuri’a 112,231. Suswam dai bai gamsu ba, don haka ya nufi kotu, yana kukan cewa an yi aringizon ƙuri’u da jirkita sakamako.

Ƙaramar kotun ta soke wa Udende ƙuri’a 51,895, shi ma Suswam ya yi asarar ƙuri’a 21,229, inda ta sake ƙidaya ƙuri'u, kuma ɗan takarar jam'iyyar PDP ya tashi da rinjayen ƙuri’a 90,590, yayin da na Udende suka koma 82,699.

Sai dai kotun ɗaukaka ƙara a ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Abimbola Adejumo ta jingine hukuncin, inda ta tabbatar da nasarar Emmanuel Udende.

Hukuncin kotun ɗaukaka ƙara dai shi ne ƙarshe a shari'ar zaɓen 'yan majalisa, bisa tanadin dokokin Najeriya.