Gwamnatin India na taron jam'iyyu kan rikicinta da Pakistan

Asalin hoton, ANI
Gwamnatin India na gudanar da wani taro da ya kunshi dukkanin jam'iyyun siyasa domin tattauna hare-haren da ta kai a kan yankin Kashmir dake karkashin ikon Pakistan , da kuma wanda ta kai ainahin cikin Pakistan din a jiya Laraba.
Pakistan dai ta ce hare -haren sun hallaka mutum 31 da suka hada da mata da yara.
Ita ma India ta ce a martanin da Pakistan ta kai mata akalla farar hula 15 ne suka mutu a bangaren iyakarta.
Wannan rikici na yanzu tsakanin kasashen biyu makwabtan juna kuma masu makaman kare-dangi na nukiliya ya faro ne, bayan da India ta kai hare-hare kan yankin Kashmir da ke karkashin ikon Pakistan da ma kwaryar ita kanta makwabciyar tata, da sunan ramuwar-gayya ta harin da wasu 'yanbindiga suka kai yankin Kashmir da ke karkashin ikon Indiyar, inda suka kashe 'yan yawon bude-idanu 26, a cikin watan da ya gabata na Afirilu.
Harin da Indiya ta zargi Pakistan da hannu a ciki, wanda ita kuma Pakistan din ta musanta.
A wani jawabi da ya gabatar cikin dare Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif, ya lashi takobin daukar fansar rayukan wadanda hare-haren da Indiya ta ce na ramuwar gayyara ne suka kashe.
India dai ta ce harin da ta kai ta kai shi ne kan yankuna da kayan 'yan ta'adda bisa bayanan sirri da ta samu masu inganci.
Mr Sharif ya bayyana ikirarin gwamnatinsa na cewa ta harno jiragen yakin Indiya biyar da wani karamin jirgin saman maras matuki a matsayin martanin ba sani ba sabo.
Sai dai India ba ta ce komai ba game da wannan ikirari na makwabciyar tata, wanda ita ma BBCba ta tabbatar ba.
Zuwa yanzu dai ba za a iya cewa ko kasahen biyu sun mayar da wukakensu kube ba a kan wannan rikici.
Amurka da Majalisar Dinkin Duniya dai na kira ga kasashen da su kai zuciya nesa, su guji ci gaba da wannan rikici.
Yanzu dai Pakistan din da India kowacce na nazarin asarar da ta yi sakamakon wannan sabani.











