Yadda wani likita dan India ya ceci rayuwar yarinya 'yar Pakistan da wuyanta ya karkace

Asalin hoton, AFSHEEN GUL/INSTAGRAM
Afsheen Gul matashiya ce ‘yar Pakistan, mai shekara 13, wadda ke fama da wata irin larura ta daban, wadda ta sa wuyanta ya lankwashe, ba ta iya dagawa.
Ta sha fama kan yadda za a yi mata magani, amma abin ya ci tura, har sai da labarinta ya kai ga wani likita a kasar India.
Wakiliyar BBC sashen BBC Urdu, Riaz Sohail, ta hada rahoto kan yadda wannan matashiya ta kai ga samun waraka.
Ga yawancin yara suna tashi ne tare da abokansu na makaranta ko na unguwa.
Wasu kuwa wata 'yar tsana ce ko kuma wani kare ko kyanwa ko kuma dai wata dabbar gida da suke sabawa da ita.
To amma ga wannan yarinya Afsheen wadda ta fito daga lardin Sindh na Pakistan abin ba haka yake ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yarinyar wadda ita ce karama a cikin 'yan uwanta bakwai, ba ta taba zuwa makaranta ba ko kuma wasa da kawaye ko abokanta ba.
Wannan ko ba don komai ba ne sai saboda wani ciwo da ta ji, lokacin da ta fado a hannun yarta lokacin tana jaririya wata goma da haihuwa, inda wuyanta ya lankwashe gaba daya gefe daya.
Iyayenta sun kai ta wajen likita wanda ya ba ta magani ya kuma daura mata wata igiya a wuyan wadda za ta taimaka mata, amma maimakon ta samu sauki abin ma sai kara tabarbarewa ya yi.
''Ba ta iya tafiya ko cin abinci ko ma magana. Sai dai kawai ta kwanta a kasa, mu yi mata komai,'' in ji mahaifiyarta Jamilan Bibi.
Kuma ta ce karfinsu ya kare ba za su iya biyan wani kudi da za a gwada yi mata wani aiki ba.
Haka kuma Afsheen ta gamu da larurar laka - sai da ta kai shekara shida ta koyi yadda za ta yi tafiya, sannan kuma ta koyi magana tana shekara takwas.
Wannan ya sa sa'o'inta suka tsere mata a rayuwa.
Tsawon shekara 12, Afsheen take cikin wannan matsananciyar rayuwa a wuri daya, wato cikin gidansu da ke garin Mithi, kusan nisan kilomita 300 daga Karachi babban birnin Pakistan.

Asalin hoton, AFSHEEN GUL/INSTGRAM
Ina ya Allah babu ya Allah, a kwana a tashi, sai wani likita a birnin Delhi na India ya samu labarinta ya kuma yi alkawarin yi mata aiki kyauta.
Dakta Rajagopalan Krishnan, kwararre a kan cutuka da raunin laka, wanda ke aiki a asibitin Apollo a Delhi, ya yi mata aiki cikin nasara.
Bayan wata hudu Afsheen tana iya tafiya da kafarta, tana iya cin abinci da kanta, har magana ma tana yi. Ta warke sumul.
A duk mako Dakta Krishnan yana duba ta ta hanyar intanet ta Skype.
Sai dai ba ta da kuzari sosai, kuma har yanzu ba ta fara zuwa makaranta ba, in ji dan'uwanta Yaqoob Kumbar.
To amma likitan ya ce za ta warware sosai a hankali.
Dan'uwan nata ya ce suna matukar farin ciki da wannan abu da likitan ya yi mata ya ceci rayuwar kanwarsu.
''Wannan likita dan'albarka ne,'' in ji shi.
Likitan ya bayyana cewa Afsheen ta ji rauni ne wanda ke hana lakarta juyawa, wanda kusan ba kasafai ake ganin irinsa ba.
Saboda haka ne wuyan nata ya yi kwanciyar magirbi, ba ta iya daga kanta.
Labarinta ya bazu a duniya a 2017 lokacin da aka yada shi a wani shafin intanet.
Tauraron dan fim na Pakistan Ahsan Khan ya yada hoton Afsheen a Facebook, inda ya roki jama'a da su taimaka.
Haka kuma an gayyaci mahaifiyar Afsheen wani fitaccen shirin talabijin wanda Sanam Baloch ke gabatarwa.
Bugu da kari wani mutum daga Amurka ya kafa asusu domin tara kudin da za a taimaka wa iyayenta su samu a yi mata aiki.

Asalin hoton, AFSHEEN GUL/INSTAGRAM
A watan Nuwamba na 2017, 'yar majalisar dokoki Naz Baloch, ta jam'iyya mai mulki a Pakistan (PPP), ta sanya sakon tuwita cewa gwamnati za ta dauki nauyin aikin da za a yi wa Afsheen.
An kai yarinyar asibitin koyarwa na jami'ar Agha Khan, wanda shi ne asibiti mai zaman kansa mafi girma a Karachi, a watan Fabrairu na 2018.
A lokacin kwararrun likitocin da za su yi mata aiki sun ce idan aka yi aikin za ta iya rayuwa za kuma a iya rasa ta.
Wannan ya sa iyayenta suka tafi da ita gida suka ce za su je su yi shawara a kai, in ji dan'uwanta Kumbar.
Bayan wani lokaci iyayen nata suka yi wa gwamnati magana a kan aikin to amma suka ga gwamnatin ba ta mayar da hankali kan maganar ba.
Ba su samu wani bayani mai karfafa guiwa ba.
Labarin Afsheen dai ya sake bayyana a kafofin yada labarai na duniya bayan da wata 'yar jarida ta Birtniya, Alexandria Thomas, ta bayar da rahotonta.
Ta kuma bayyana irin halin da iyayenta suke ciki na rashin kudin da za su iya biya na yi mata aiki.
'Yar jaridar ta kuma hada iyayen da Dakta Krishnan a Delhi, wanda ya yi magana da yayan Afsheen, Mista Kumbar.
Ya gaya masa cewa yana son ya taimaka wa Afsheen.
Daga nan aka shirya aka kai Afsheen India a watan Nuwamba na shekarar da ta wuce, karkashin wata kungiya mai taimaka wa yara, Darul Sukoon.

Asalin hoton, AFSHEEN GUL/INSTAGRAM
Mista Kumbar ya bayyana irin mawuyacin halin da suka shiga na neman yi wa kanwar tasa aiki, baya ga rashin kudi.
Ya ce ya yi ta faman tuntubar likitoci daban-daban, amma babu wanda ya nuna damuwa kamar Dakta Krishnan.
A karshe dai suka dogara daga asusun tallafin da aka samar ta intanet, wajen samun kudin aikin.
Ya kuma ce likitan ya sheda musu cewa zuciya ko huhunta, ka iya tsayawa da aiki a lokacin tiyatar.
To amma duk da haka likitan ya karfafa musu zuciya a kan aikin.
A karshe dai an yi wa Afsheen aiki a watan Fabrairu, bayan wasu kananan ayyukan da aka yi mata guda biyu, kafin a yi babbar tiyatar.
Dakta Krishan ya gaya wa BBC yadda shi da ayarin ma'aikatansa suka yi wannan tiyata ta tsawon sa'a shida, wadda a karshe ta kai ga samar da lafiya ga Afsheen.

Asalin hoton, AFSHEEN GUL/INSTAGRAM
Bayan an kammala tiyatar cikin nasara, Dakta Krishnan, ya gaya wa 'yan jarida cewa da ba a yi aikin ba, to da Afsheen ba za ta yi tsawon rayuwa ba.
To amma yanzu ga shi tana murmushi da magana, in ji yayanta Mista Kumbar, a lokacin da ya sanya wani hotonta a Facebook, a watan nan na Yuni, ranar jajiberin Babbar Sallah.










