Grealish na iya maye gurbin Wirtz a Leverkusen, Sporting ta fusata Gyokeres

Jack Grealish

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Ɗanwasan Manchester City Jack Grealish mai shekara 29 na iya zama wanda zai maye gurbin ɗanwasan tsakiyar Jamus Florian Wirtz idan ya bar Bayer Leverkusen. (Sun)

Ɗanwasan Sweden Viktor Gyokeres ya fusata ganin yadda kulob ɗinsa Sporting ya yi mi ara koma-baya kan yarjejeniyar da ta ce ɗanwasan mai shekara 27 na iya barin ƙungiyar a bazara kan fam miliyan 67. (Record - in Portuguese)

Manchester City ta amince ta ƙulla yarjejeniyar fam miliyan 34 da Lyon don ɗanwasanta ɗan asalin Faransa mai shekara 21 Rayan Cherki. (Times - subscription required)

Arsenal ta zaƙu ta ɗauki golan Chelsea ɗan asalin Sifaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 30 kan fam miliyan 5. (Sky Sports)

Burnley ta ƙayyade darajar ɗanwasanta Maxime Esteve mai shekara 23 kan fam miliyan 50 daidai lokacin da Bayern Munich, wadda ke ƙarƙashin jagorancin tsohon kocin Burnely ɗin Vincent Kompany, ke hanƙoran sayen shi. (Football Insider)

Ɗanwasan Paris St-Germain, Bradley Barcola mai shekara 22 ya zama wanda Bayern take mararin ɗauka a wannan bazara, yayin da ɗanwasan Atletico Madrid Nico Williams, shi ma mai shekara 22, ya kasance cikin zaɓinta. (Sky Sport Germany - in German)

PSG na son Ilya Zabarni na Bournemouth sai dai ƙungiyar na neman a biya ta fam miliyan 59 kan ɗanwasan na Ukarine. (L'Equipe - in French)

Tottenham ta ƙara ƙaimi don ɗauko ɗanwasan Bournemouth Antoine Semenyo yayin da Manchester United ke ci gaba da nuna sha'awa kan ɗanwasan gaban na Ghana mai shekara 25. (Sky Sports)

Newcastle United na zawarcin ɗanwasan Ghana Mohammed Kudus mai shekara 24 daga West Ham bayan da ta rasa damar sayen ɗanwasan Brentford Bryan Mbeumo. (Football Insider)

West Ham na duba yiwuwar yin musayar Kudu da Chelsea yayin da West Ham ɗin take a shirye ta sakar wa ɗanwasanta Nayef Aguerd marar ficewa daga ƙungiyar a bazara kan fam miliyan 25. (Teamtalk)

Manchester City a shirye take ta ɗauko golan Chelsea Marcus Bettinelli mai shekara 33 a dalilin adabo da Scott Carson ya yi daga ƙungiyar. (Telegraph - subscription required)

Tottenham ta zama kulob na baya-bayan nan da ya nuna sha'awarsa kan ɗanwasa Dorgeles Nene, mai shekara 22 da ke bugawa Red Bull Salzburg ta Bundesliga. (Teamtalk)