Za a gwada lafiyar Tijjani a Man City, Arsenal na shirin ɗaukar Arrizabalaga

Tijjani Reijnders

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tijjani Reijnders
Lokacin karatu: Minti 2

Tijjani Reijnders ya kusa komawa Manchester City, Newcastle United ta mayar da hankali kan dan wasan gaban Brighton Joao Pedro, Brentford na iya neman kocin Ipswich Town Kieran Mckenna idan Thomas Frank ya tafi.

Za a gwada lafiyar dan wasan tsakiya na Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 26, a Manchester City nan gaba a yau, don kammala komawarsa kungiyar daga AC Milan. (Sky Sports)

Hungary ta hutar da dan wasan baya na bangaren hagu na Bournemouth Milos Kerkez daga taka leda tawagar kasar, yayin da dan wasan mai shekaru 21 ya kusa komawa Liverpool. (Mirror)

Newcastle United na shirin kara kaimi wajen zawarcin dan wasan gaban Brighton da Brazil Joao Pedro, mai shekara 23, bayan da alamu suka nuna sun kasa dauakr dan wasan Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, wanda ake sa ran zai koma Manchester United daga Brentford. (Telegraph)

Kocin Ipswich Town Kieran McKenna na cikin jerin sunayen masu horarwar da ake sa ran Brentford za ta dauka don ya gaji Thomas Frank, wanda ake ganin zai kasance kan gaba wajen maye gurbin Ange Postecoglou da aka kora a Tottenham. (Talksport)

Dan wasan gaba na kasar Portugal Rafael Leao ya shaidawa AC Milan cewa yana son barin kungiyar, wadda ke neman akalla yuro miliyan 70 (£59m) kan dan wasan mai shekaru 25, wanda yana daya daga cikin wadanda Bayern Munich ke zawarci. (Florian Plettenberg)

Chelsea na shirin komawa da tayi na biyu kan golan Faransa Mike Maignan, mai shekara 29, bayan tayin farko, wanda ya yi kasa da farashin da AC Milan ta Serie A take nema. (Calciomercato Italia)

Juventus ta cimma yarjejeniya da Paris St-Germain don tsawaita zaman aron dan wasan gaban Faransa Randal Kolo Muani, domin dan wasan mai shekaru 26 ya buga wa kungiyar ta Seria A gasar cin kofin duniya ta kungiyoyin Fifa. (Sky Italia)

Dan wasan gaban Napoli na Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 26, ya amince da tayin kwantiragi daga kungiyar Al-Hilal ta Saudi Pro League. (Sky Italia)

Fenerbahce ta bi sahun takwararta ta Galatasaray ta Turkiyya da ke son siyan dan wasan Jamus Leroy Sane mai shekaru 29, wanda har yanzu bai amince da tayin sabon kwantaragi da Bayern Munich ba. (Sky Sports Germany)

Bayern Munich ta cimma yarjejeniya da Bayer Leverkusen don siyan dan wasan baya na Jamus Jonathan Tah, mai shekara 29, kafin kwantiraginsa ya kare a ranar 30 ga watan Yuni domin ya samu damar buga gasar cin kofin duniya ta kungiyoyin Fifa. (Fabrizio Romano)

Arsenal na shirin dauko golan Chelsea Kepa Arrizabalaga, mai shekara 30 (Evening Standard)