Madrid na neman yi wa Arsenal ta-ɓare kan Zubimendi, Al-Hilal na son Sancho

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool na shirin bayar da fam miliyan 118 don siyan Florian Wirtz na Bayer Leverkusen, Everton na zawarcin dan wasan tsakiya na Manchester City Jack Grealish sannan Real Madrid za ta iya yin hamayya da Arsenal kan Martin Zubimendi.
Liverpool na shirin yin tayin karshe na fam miliyan 118, gami da kari, kan dan wasan Jamus Florian Wirtz, mai shekara 22, bayan Bayer Leverkusen ta ki amincewa da tayin fan miliyan 113. (Mail)
Everton na sha'awar dan wasan tsakiya na Ingila Jack Grealish, amma da alama sai dai ya je a matsayin aro, saboda albashin dan wasan mai shekaru 29 a Manchester City. (Mail)
Real Madrid za ta yi yunkurin karshe na sayen dan wasan tsakiyar Real Sociedad, mai shekara 26, Martin Zubimendi, mai shekara 26, wanda ke dab da komawa Arsenal. (AS in Spanish)
Har yanzu Arsenal ba ta cimma yarjejeniya da RB Leipzig ba kan dan wasan gaban su na Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 22, amma an shirya tattaunawa ta gaba. (Sky Germany)
Dan wasan gaban Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22, ya ce baya tunanin barin Manchester United, duk da ana alakanta shi da komawa Inter Milan. (Talksport)
Dan wasan tsakiya na Ingila, Myles Lewis-Skelly, mai shekara 18, na shirin sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da Arsenal duk da sha'awar da Real Madrid ta nuna (Football Insider)
Borussia Dortmund ta ki amincewa da tayin da Chelsea ta yi na Yuro miliyan 35 (£29.5m) kan dan wasan Ingila Jamie Gittens, wanda farashinsa ya kai Yuro miliyan 50 zuwa 60 (£42-£50m) kan dan wasan mai shekaru 20. (Sky Sports)
Chelsea ta shirya biyan AC Milan har Yuro miliyan 15 (£12.6m) kan golan Faransa Mike Maignan mai shekaru 29. (Sky Sports)
Dan wasan bayan Verona da Italiya Diego Coppola, mai shekara 21, yana jan hankalinBournemouth da Como a wannan bazarar. (Football Insider)
Dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen ya ki amincewa da yarjejeniyar da ta kai Yuro miliyan 30 (£25.3m) a duk kakar wasa daga Al-Hilal, wadda ta amince ta biya Napoli kudin dan wasan mai shekaru 26 Yuro miliyan 75 (£63.2m). (Football Italia)
Dan wasan Ingila da Manchester United Jadon Sancho, mai shekara 25, yana daya daga cikin 'yan wasa da dama da Al-Hilal ke tunanin dauka a bazara. (Foot Mercato)
Hukumar kwallon kafa ta Italiya na zawarcin tsohon kocin Chelsea, da Leicester City da Roma Claudio Ranieri domin ya gaji Luciano Spalletti a matsayin kocin Italiya. (Football Italia)











