Da gaske ambaliya ta kusa shafe gadar Third Mainland ta Lagos?

Wani labarin ƙarya cewa ambaliyar ruwa na dab da shafe gadar Third Mainland da ke Lagos a Najeriya ya yaɗu tamkar wutar daji.

Najeriya na fama da mummunar ambaliar ruwan da ba a ga irinta ba a cikin gwamman shekaru, lamarin da ya shafi al'ummomi da dama da ke kusa da Kogin Neja da na Binuwai.

Ambaliyar ta yi sanadin mutuwar a ƙalla mutum 600.

Sashen binciken gaskiya na BBC ya bi diddigin inda labarin cewa ambaliyar ta kusa shafe gadar ya fito, wanda aka fara gani a wani bidiyo mai tsawon sakan 13 da aka yaɗa a Tuwita ranar 21 ga Oktoban 2022 da ƙarfe 8.15 na dare agogon ƙasar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

An sake yaɗa bidiyon sau tara da tsokaci bakwai a ƙarƙashinsa.

An ɗauki bidiyon ne a cikin wata mota a yayin da take tafiya a kan titin Gadar Third Mainland, wanda yanayin da aka ɗauki bidiyin ta gefe ne ya sa za a ga kamar ruwan teku ya fara haurawa kan gadar.

Wani fitaccen mai barkwanci Williams Uchemba ma ya wallafa wani bidiyo daga kan gadar yana ikirarin cewa ruwan teku yana toroƙo.

Wani saƙon kuma da aka wallafa a Facebook na ikirarin cewa wani hoto da aka ɗauka a kwana-kwanan nan na nuna yadda ruwan teku ke toroƙo yana hawa kan gadar.

This view was also shared by some Twitter users, further spreading this disinformation.

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Wannan hoton ne wasu ke yaɗawa cewa ruwa ya fara hawa kan gadar Third Mainland
This view was also shared by some Twitter users, further spreading this disinformation.

Asalin hoton, Twitter

Waɗannan saƙonnin suna ikirarin cewa wani hoto da aka ɗauka a baya-bayan nan na nuna ruwan tekun da ke Ikko na toroƙo hatr yana taɓa gada, sai dai babu wata ƙwaƙƙwarar hujja.

Haka ma ake faɗa a cikin wancan bidiyon na sama.

Amma wani sharhi da aka yi kan hoton da suka yaɗa ɗin na nuna cewa yawan ruwan tekun yana iyakar dirkar gadar ne.

Wani bayanin kuma kan hoton na tabbatar da cewa ba sabon hoto ba ne, tun shekarar 2020 aka ɗauke shi aka wallafa a wani labari mai alaƙa da Gadar Third Mainland ɗin.

Third Mainland

Asalin hoton, Twitter

Sashen binciken gaskiya na BBC ya je har wajen gadar ta Third Mainland don gane wa idonsa kuma ya ga cewa ruwan tekun bai ma haura farko-farkon ginshikan gadar, inda dama yawanci ruwan ba ya wuce nan.

Hakan na nufin waɗancan hotunan da aka yaɗa da Facebook da Twitter da Instagram da kuma WhatsApp duk na ƙarya ne.

An ɗauki wadannan hotunan da ke ƙsa ne ranar 26 ga watan Oktoban 2022 da ƙarfe 10 na safe kuma suna nuna ainihin yanayin da gadar ke ciki.

Third Mainland Bridge

Asalin hoton, Twitter

Third Mainland

Asalin hoton, Twitter

Labaran ƙaryar kan batun gadar sun jawo fargaba a tsakanin mutane a shafukan sada zumunta, inda mutane ke tsoron cewa ambaliyar ruwa na dab da shafe su.

Tweep

Asalin hoton, Twitter

Tweep

Asalin hoton, Twitter

Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na jihar Lagos Tunji Bello, ya fitar da sanarwar gargaɗi cewa wasu sassan jihar ka iya yin ambaliya sakamakon toroƙon da ruwan tekun ke yi.

Tun da fari gwamnatin jihar ta fitar da sanarwa tana bai wa mazauna yankunan da ke kusa da Kogin Ogun shawarar yadda za su tunkari ambaliya.

Wadannan yankuna yawanci suna fuskantar barzanar ambaliya saboda ruwan da ake sakowa daga Madatsar Ruwan Oyan da ke jihar Kogi.

Ana sakin ruwan Kogin Ogun ɗin ne zuwa cikin Tekun Lagos.

A yayin da hasashen yanayi ke nuna cewa yawan ruwan teku zai ƙru saboda mamakon ruwan sama da sakin ruwan Madatsar Ruwan Oyan, babu wata hujja cewa yawan ruwan tekun ya kai wannan da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta.

Third Mainland

Asalin hoton, Others

Gadar Third Mainland ita ce ta biyu mafi girma a Afirka. An fara gina ta ne a shekarar 1980 aka kammala a 1990.

Gadar mai tsayin kilomita 12 ita ce mahaɗar yankin Lagos Island da ke kan ruwa zuwa na Lagos Mainland da ke kan ƙasa.

Ambaliyar ruwa a kan wannan gada zai iya kawo naƙasu ga tattalin arzikin Lagos, babbar cibiyar kasuwancin Najeriya.