Barnar da ambaliya ta yi a Najeriya

Flood

Kamar yadda ake ta fama da barnar ambaliyar ruwa a kasashe da dama a fadin duniya, Najeriya ma na daga cikin kasashen da wannan iftila’i ke shafa.

Ko a ranar Litinin ma hukumomi sun ce ambaliya ta kashe mutum 372 a jihohi 33 na Najeriya da kuma Abuja babban birnin kasar a cikin watanni takwas.

Jihar Jigawa da ke Arewa maso Yammacin Najeriyar na daga cikin jihohin da bala'in na ambaliya ya fi shafa.

A ranar 14 ga watan Agusta hukumar agajin gaggawa ta jihar ta bayyana wa manema labarai cewa mutum 50 sun mutu kuma ambaliyar ta rusa dubban gidaje, abin da yasa mutane da dama suka rasa matsugunai.

A lokacin BBC ta tattauna da mahaifin da ya rasa 'ya'yansa uku a Hadejiya, bayan da ambaliya ta rusa katangar dakin da suke bacci a ciki.

Dama tsawon shekaru jihar Jigawa ta sha fuskantar ambaliya wadda ke zuwa da rasa rayukan al'umma da dama da lalacewar gidaje da hanyoyi.

Yanzu haka an samar da sansanonin wucin gadi ga wadanda suka rasa matsugunai a jihar, yayin da wasu suka nemi mafaka a gine ginen gwamnati.

BBC Hausa tana son jin labaran yadda ɓarnar ambaliyar ruwa ta shafe ku – idan har mun ga labarinku mai ma’ana ne, to za mu tuntuɓe ku don yin hira da ku da kuma wallafa shi.