Ana fargabar karuwar ambaliya a Jigawa bayan mutuwar mutum 50

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ba da agajin gaggawa a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta bukaci mazauna wuraren da ke kusa da koguna da sauran hanyoyin ruwa da su gaggauta sauya wurin zama.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar ƙarin ambaliya a damanar bana.
Hukumar ta ce zuwa yanzu ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 50, tare da raba dubbai da matsugunansu a sassan jihar.
A cewarta hasashe ya nuna za a ci gaba da samun mamakon ruwan sama a 'yan kwanakin nan, sannan kuma za a sako ƙarin ruwa a kogin da ya hada Hadejiya da Jama'are.
Dama hukumar da ke lura da hasashen yanayi a Najeriya ta yi gargadin cewa za a sami ruwan sama sosai musamman a Arewacin kasar.
Kazalika jihar Jigawa na daga cikin jihohin Arewacin Najeriyar da suka fuskanci ambaliya a baya bayannan, da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Ko a makon da ya gabata BBC ta tattauna da mahaifin da ya rasa 'ya'yansa uku a Hadejiya, bayan da ambaliya ta rusa katangar dakin da suke bacci a ciki.
Rahotanni sun nuna cewa kawo yanzu mutum 50 ne ambaliyar tayi ajalinsu, haka ma darurruwan gidaje sun rushe.
Tuni hukumomin Najeriya suka fara aikewa da tallafin gaggawa ga wadanda suka rasa matsugunansu.
Honorabul Yusuf Sani, wanda shine Shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar ta Jigawa ya fada wa BBC cewa an shafe kwana uku ana ruwa ba dare ba rana a duka fadin jihar.
''Wannan ruwan da aka shafe kwana uku ana yi duka kananan hukumomi 27 babu inda ba a samu wannan ruwan saman ba. Kuma gaskiya wannan rusau din ko'ina an same shi", in ji Yusuf Sani.
Ya kara da cewa, ''mutanen da ke zaune kan hanyar ruwa da kuma kusa da kogi mun fada musu su tashi daga wurin.''
Shugaban hukumar ya kuma ce sun samar da sansanoni na wucin gadi, da yanzu haka ke dauke da sama da mutum 1,000 da suka rasa gidajensu sanadiyyar ambaliya.
A shekarun baya-bayan nan jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya ta fuskanci ambaliya fiye da sauran jihohin kasar.











