Dalilin da ya sa Musulmai suka tsani Salman Rushdie

Salman Rushdie

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Salman Rushdie ya daɗe yana rayuwa a ɓoye saboda barazanar kashe shi

Littafin “The Satanic Verses” da Salman Rushdie ya rubuta ya jawo masa tsana da kuma barazanar kisa tsawon shekara 30, saboda yadda Musulami a faɗin duniya suka ce ya yi ɓatanci ga Annabi Muhammadu S.A.W.

Harin da aka kai wa marubucin ranar Juma’a ya faru ne shekara 33 bayan samun barazanar kisa ta farko a rayuwarsa.

Maharin ya caccaka masa wuƙa a wuya ranar 12 ga watan Agusta lokacin da yake kan dandamali don gudanar da jawabi a wani taron marubuta a birnin New York na Amurka.

Marubucin mai shekara 75 ɗan Birtaniya da aka haifa a Indiya, ya rubuta litattafan da suka karɓu a duniya.

Littafinsa na biyu mai suna "Midnight's Children" ya ci kyautar Booker Prize a 1981, wanda ake kallo a matsayin ɗaya daga cikin ƙagaggun labarai mafiya ƙayatarwa da aka rubuta da harshen Ingilishi.

Sai dai kuma littafin "The Satanic Verses" wanda shi ne na huɗu da ya rubuta, shi ne ya fi haddasa cecekuce a faɗin duniya, wanda al’ummar Musulmai ke bayyanawa da cewa ɓatanci ne ga Annabi Muhammadu S.A.W.

Ladan da za a bai wa wanda ya kashe Rushdie

Indiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayan rubuta littafin na “The Satanic Verses”, wanda ke nufin “Ayoyin Shaiɗan”, Shugaban Addini na ƙasar Iran Ayatollah Khomeini ya ba da fatawar kashe Rushdie a 1989.

Kazalika, Khomeini ya yi tayin bai wa duk wanda ya kashe shi kyauta ko ladan dala miliyan uku.

Zuwa shekarar 1998 gwamnatin Iran ta daina yaɗa fatawar kuma ta nesanta kanta daga batun, kodayake wasu rahotanni na cewa an ci gaba da yaɗa shi a 2016.

Barazanar kisa da aka dinga aika wa Rushdie ta sa ya shafe shekara kusan 10 yana gudanar da rayuwarsa a ɓoye. Gwamnatin Birtaniya ta ba shi kariya ta hanyar ba shi rakiyar jami’an tsaro.

"The satanic verses" – “Ayoyin Shaiɗan”

Littafin “The Satanic Verses”

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Littafin “The Satanic Verses” ya jawo tashin hankali a sassan duniya tun bayan wallafa shi a 1988

Littafin “The Satanic Verses”, ƙagaggen labari ne da ya fusata Musulmai a faɗin duniya saboda abin da suka kira ɓatanci ga addinin.

Daga cikin abin da ya fi ɓata wa Musulmai rai shi ne yadda ake kiran wasu karuwai biyu a littafin da sunan matan Annabi.

Sunan littafin ya samo asali ne daga abin da Rushdie ya yi iƙirari a littafin cewa Annabi ya goge wasu ayoyi biyu da ya ce sun samo asali ne daga shaiɗan.

A littafin, an ba da labarin wasu jarumai ne ‘yan Indiya da suka tsira daga wani hatsarin jirgin sama bayan an kai musu hari.

Haka nan, an cakuɗa ƙagaggen labarin da kuma wasu abubuwa da suka faru a rayuwar Annabi Muhammadu, wanda Musulmai ke matuƙar girmamawa.

Martanin da ya biyo bayan rubuta littafin

Masu zanga-zanga a Faransa a 1989 kan littafin "The Satanic Verses"

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu masu zanga-zanga ke nan a birnin Paris na Faransa kan littafin a shekarar 1989
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Indiya ce ƙasa ta farko da ta haramta sayar da littafin. Sai Pakistan da Afirka ta Kudu da suka bi sahu kafin daga baya sauran ƙasashen Musulmi da dama su yi hakan.

Sai dai wasu sun yabi littafin, har ma aka dinga ba shi kyautuka daban-daban.

Amma an ci gaba da nuna ɓacin rai game da littafin, inda aka zanga-zanga ta biyo baya a wasu sassa na duniya.

A watan Janairu na 1989, Musulmai a birnin Bradford na Birtaniya suka yi bikin ƙona kwafin littafin, su kuma shagon WHSmith suka daina nuna littafin.

A lokacin, Rushdie bai yarda cewa ya yi ɓatanci ga addinin Musulunci ba.

A birnin Mumbai na Indiya, inda aka haife shi, an kashe mutum 12 yayin zanga-zanga. An jefi ofishin jakadancin Birtaniya da duwatsu.

Wasu shugabannin Musulmai sun nemi a kai zuciya nesa, wasu kuma suka nuna goyon baya ga umarnin Ayatollah. Amma Amurka da Faransa da sauran ƙasashen Turai sun yi Allah-wadai da umarnin kisan.

Daga baya kuma, Rushdie wanda ke ɓoye tare da iyalinsa, ya nuna nadama kan abin da ya haifar ga Musulman duniya, amma Ayatollah bai janye kiran da ya yi ba na kisan marubucin.

An kai wa ofisoshin kamfanin Viking Penguin hari a Landan da New York, wanda shi ne ya wallafa littafin. A gefe guda kuma, littafin ya ci gaba da shahara a duniya.

A nasu martanin, ƙasashen Turai da ke adawa da zanga-zangar da Musulman ke yi sun janye jakadunsu daga Iran.

Sauran marubuta littafin da aka kashe

Ba marubucin littafin "The satanic verses" ne kawai ya fuskanci fushi ba, waɗanda suka fassara shi zuwa wasu harsuna sun gamu da ajalinsu sakamakon yin hakan.

 An ga gawar wani mai mafassarin littafin zuwa harshen Japan bayan an yanka shi a wata jami’a da ke birnin Tokyo a watan Yulin 1991.

‘Yan sanda sun ce mafassarin mai suna Hitoshi Igarashi ya yi aiki a matsayin mai shirin zama farfesa a fannin al’adu, an caccaka masa wuƙa a wajen ofishinsa na Jami’ar Tsukuba. Har yanzu ba a gano wanda ya kashe shi ba.

A wannan watan dai, an sossoka wa mafassarin harshen Italiya, Ettore Capriolo, wuƙa a gidansa da ke Milan, amma ya tsira daga harin.

Shi ma mafassarin harshen Norway, William Nygaard, an harbe shi a 1993 a wajen gidansa da ke birnin Oslo – shi ma bai mutu ba a harin.