KU BA MU LABARANKU: Ta yaya ambaliyar ruwa ta shafe ku a bana?
Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya ta ce mutum 372 ne suka rasa sayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a jihohi 33 da kuma babban birnin tarayyar Abuja a ƴan watannin da suka wuce.
Kazalika ambaliyar ta rusa dubban gidaje da lalata gonaki da amfanin gona a fadin kasar. Shin kuna cikin mutanen da suka yi rashin ƴan uwa ko dangi sakamakon ambaliyar? Ba mu labarin yadda lamarin ya faru – idan har mun ga labarinku mai ma’ana ne, to za mu tuntuɓe ku don yin hira da ku da kuma wallafa shi.