Da gaske Jihar Legas na nutsewa cikin ruwa?

"Tun lokacin da aka haife ni nake rayuwa a nan. A shekaru da suka gabata, mun ga igiyar ruwa. Ka dubi abin da ta yi wa wannan al'umma,'' in ji Monday Idowu, wani mazaunin bakin teku a Lafiaji, da ke Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya.
Muna tsaye ne a kan wurin da a shekara uku da suka gabata ya kasance bakin teku. Wasu bangarorin wurin na dauke da tushe da aka yi amfani wajen gina gidaje.
Tun da a yanzu ya kasance ba bakin teku ba ne, mene ne shi?: ''A 2018, lokacin da nake shirin tafiya aiki, a idona ruwa ya yashe gidana,'' a cewar Monday. ''Cikin dakika kadan, igiyar ruwa daga tekun Atlantika, ta ruguza gidana mai dakuna uku.
Duk lokacin da na kalli teku a yanzu, wani radadi nake ji. Ba na son ma na kalli bakin teku.
Wani bincike da wata cibiyar bincike ta yanayi ta wallafa, ya nuna cewa biranen da ke gabar teku a wasu sassan duniya za su iya nutsewa idan ruwan teku ya ci gaba da tuttudowa.
Me hakan yake nufi ga Legas? Wata barazana birnin ke ciki?
Legas ta kasance jiha ce da aka kirkiro tsakanin tsibirai na ruwa - sannan bakin ruwa na Lafiaji na daya daga cikin tsibiran. Wadanda suke zaune a tsibirin sun shaida mani cewa igiyar ruwa ta shafi gidajensu a lokuta da dama.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar masana binciken igiyoyin ruwa, al'ummomi da ke rayuwa a gabar teku, za su iya fuskantar karuwar guguwa daga teku tsakanin watannin Afrilu da Yuni da Agusta da kuma Oktoba.
"Idan abubuwa suna cikin yanayi mai kyau, igiyoyin ruwa na kai matakin mita 0.8 zuwa 0.78.
Sai dai lokacin da aka samu kakkarfar igiyar ruwa, ruwan da ke cikin teku, na yin sama zuwa mita hudu da ruwa,'' a cewar Dr Regina Folorusho wata darakta a sashen kula da yanayi a cibiyar nazarin ruwa ta Najeriya.
Ana danganta rugujewar gidaje saboda karuwar tuttudowar ruwa a bakin teku. Lokacin da aka samu igiyar ruwa mai karfi, takan kai matakin mita biyu ko fiye a saman ruwa.
Mun riga mun fada cewa ya kan kai mita hudu, don haka me ya sa muke bukatar haka?
Binciken baya-bayan nan ya nuna cewa akalla ana rasa mita 35 na ruwa a bakin teku kowace shekara. A birnin Legas ko Jihar baki daya?
"Na kasace a wannan masana'antar sama da shekara talatin, kuma ban taba ganin ruwa ya tuttudo zuwa sama kamar yadda muke gani a yanzu ba,'' in ji Dr Folorunsho.
Wane hasashe ake da shi na cewa ruwan teku zai tuttudo ya zauna wuri daya na lokaci mai tsawo - wannan bangare na nufin ambaliyar ruwa da ake samu a-kai-a-kai.
Me ya sa hakan ke faruwa?
Gwamnatin Jihar Legas ta gina jinga a cikin teku domin kaucewa lalata karin kayayyaki a bakin tekun. Jingar ya hada da zuba duwatsu masu karfi a cikin wani dogon layi a bakin ruwan.
Sai dai, duk wani sauyi na yadda ruwa ke tafiya cikin teku, hakan zai yi tasiri kan al'ummomi da ke zaune a bakin teku wadanda kuma ba su da kariya. Shin suna kara tsananta matsalar ne? Me suka cimma takamaimai?
"Babu wanda zai iya dakatar da gudanar ruwa duk da abubuwan kariya da aka sanya. Alal misali, wadannan abubuwan kariya da aka sanya, shi ya sa bakin teku a tsibirin Victoria ya yi ambaliya wadda ta kai ga sun sauya da aikin bakin tekun Atlantika.
Don haka, kowane irin abu ka saka a bakin teku, zai janyo tuttudowar wani bangare na ruwan. Me hakan ke nufi?,'' a cewar Dr Folorunsho.

Ana kuma danganta matsaloli da ake samu kan kamfanonin gine-gine irin su Eko Atlantic da suka yi gini a kan wani wuri kusa teku.
Masana sun ce in har ba a kafa dokoki da za su takaita irin gine-ginen da ya kamata a yi kusa teku ba, da wuya a kare mutane da ke rayuwa kusa da bakin teku wadanda suke cikin barazana ta rayuwarsu.
"A can baya, an samu koma baya kan dokoki da aka kafa, inda ake barin mutane su yi gini mai nisan mita 100 da gabar teku, inda ba za ka gina komai ba ta bangaren arewaci. Amma a yanzu, mutane basu damu da hakan ba, suna gine-gine yadda suke so,'' a cewar Dr Folorunsho.
A lokuta da dama, BBC ta nemi ji daga bakin gwamnatin Jihar Legas , sai dai babu wani martani da ta samu.
Karuwar tuttudowar ruwa wani batu ne da ke shafar al'ummomi daban-daban a fadin duniya, inda masana suke gargadin cewa muddin ba a sanya tsare-tsare na kawo sauyi ga al'ummomin baya, tuttudowar da ruwa ke yi zai ci gaba da daidaita al'ummomi.











