Kunle Adeyanju: Dan Najeriyar da ya je Lagos daga London a kan babur ya fadi abubuwan da ya gani a kan hanya

Asalin hoton, @lionheart1759/Twitter
"Sahara ba wurin zama ba ne ga mutum, amma sahara ba ta da daɗin zama domin zafi na iya kashe mutum haka ma ruwan sama, ko kuma tsananin zafi ya kashe mutum. Yanayin sahara ba sauki"
Wannan ne abin da Kunle Adeyanju ya shaida wa sashen BBC Pidgin yayin da ya bayyana hatsarin tafiyar da ya yi daga London zuwa Legas.
Adeyanju wanda ya ratsa ƙasashe 14 ya ce yankin sahara ne ya fi shan wahala.
Ya ce ya ɗauke shi kwana bakwai kafin ya tsallake yankin Sahara.
Adeyanju ya fara wannan balaguron ne a ranar 19 ga Afrilu domin wayar da kai da kuma samar da kuɗi na yaƙi da Polio a Afirka, kuma ɗan Najeriyar a iso Legas ne a ranar Lahadi 29 ga Mayu a tafiyar kilomita 12,000.
Ya shaida wa BBC cewa yana son amfani da wannan damar domin wayar da kan al'umma cewa har yanzu akwai Polio wanda ya kamata ƙasashen Afirka su yi ƙoƙarin magancewa.
Ya ce ya gana da mata da ƙananan yara a wuraren da ya tafi a balaguronsa domin wayar da kansu game da ciwon.
'Tafiyar akwai wahala'

Asalin hoton, @lionheart1759/Twitter
Ya ce kafin ya fara balaguron, ya san cewa ba abu ba ne mai sauki.
"Na san cewa tafiyan ba za ta kasance mai sauƙi ba. Abin da kawai ke ba ni ƙwarin guiwar ci gaba da tafiyar shi ne saboda shirin da na yi.
"Na yi shiri sosai. Ya ɗauke ni tsawon shekara ina shirin wannan balaguron, in ji Adeyanju.
Ya ce daga cikin shirinsa shi ne ya gano inda asibiti da ofishin ƴan sanda suke a hanyar da zai bi.
Sannan ya ce kafin fara balaguron sai da ya koyi aikin kanikanci da gyran taya don idan har akwai matsala zai iya gyarawa da kansa.
Ba ni ne na farko ba

Asalin hoton, @lionheart1759/Twitter
Adeyanju ya ce ba shi ne na farko ba da ya taba hawa tsaunin Kilimanjaro da kuma hawa keke daga Lagos zuwa Ghana.
Ya ce ya samu goyon baya daga iyalinsa.
"Iyalina sun san ni wane irin mutum ne domin ba wannan ne karon farko ba da na yi irin wannan. Na taba hawa tsaunin Kilimanjaro. Sau biyu ina hawa, a 2008 da 2009. Na hau keke daga Lagos zuwa Ghana," in ji Adeyanju.
Goyon bayan mutane saboda manufar yaki da Polio

Asalin hoton, @lionheart1759/Twitter
Adeyanju ya ce goyon bayan da ya samu daga balaguron ya wuce tunaninsa.
Ya ce ya hadu da ƴan sa-kai da za su yi diga wa yara rigakafin polio.
Adeyanju ya shaida wa BBC cewa mutane na tallafawa da kudi amma kuma ƴan Rotary Club ke karɓar kudi.
Yadda ya yi balaguron

Asalin hoton, @lionheart1759/Twitter
Bayan ɗan Najeriyar ya fara balaguron a ranar 19 ga Afirlu, ya ce ya hau babur dinsa daga London zuwa Dover har zuwa Faransa.
"Dover ne kan iyakar Birtaniya a London. Akwai ruwa a wurin, ni da babur dina muka shiga jirgin ruwa.
"Na biya fam 30 na hawa jirgin ruwa, sannan na biya wa babur dina fam 40. tafiyar awa ɗaya ne da minti 30 a jirgin ruwa. Mun sauka a Calais a Faransa," kamar yadda Adeyanju ya shaida wa BBC.
"Daga Calais, Adeyanju ya ce ya tuƙa babur ɗinsa zuwa Brugge inda dare ya yi masa ya kwana. Daga Brugge, ya shiga Girona a Spain, inda ya shiga Valencia zuwa Cartegena, daga nan kuma ya tsallaka iyakar Spain kuma kan iyakar turai.
"Daga nan ya shiga jirgin ruwa a Bahar Rum, jirgin ya ratsa inda ake kira Gibraltar kuma ya biya fam 82 a tafiyan minti 40. Mun tsallaka muka shiga Morocco.

Asalin hoton, @lionheart1759/Twitter
Jirgin ya ajiye Adeyanju Tangier, daga nan ya shiga Rabat zuwa Casablanca inda daga nan ya shiga Marrakesh.
Daga Marrakesh Adeyanju ya hau babur zuwa Agadir har zuwa inda ya fita kasar Morocco. Ya ci gaba da tafiya har zuwa Mauritania zuwa Lagos.
Mene ne mataki na gaba ga Adeyanju?

Asalin hoton, @lionheart1759/Twitter
Adeyanju ya ce abin da zai yi a gaba shi ne zai yi balaguro saman babur daga Lagos zuwa Isra'ila daga nan zai shiga ƙasashen yankin Asiya.
Ya ce zai tafi Tibet da kuma hawa tsaunin Everest.
"Wannan ne burina na gaba. Wannan ina fatan zai faru ne nan da shekara biyu, in ji Adeyanju.











