Al Hilal na zawarcin Richarlison, Everton na son Iheanacho, Arsenal za ta sayar da Ramsdale da Nketiah da Rowe

Richarlison

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Richarlison

Al-Hilal wadda ta lashe gasar Zakarun Saudi Pro League na da kwarin gwiwar sayan dan wasa mai kai hari na Tottenham da Brazil Richarlison a wannan bazara, yayin da Spurs ta bude kofofinta ga kungiyoyin da ke son dan wasanta mai shekara 27 (Mail)

Watakila Tottenham ta maye gurbin Richarlison da dan wasan Crystal Palace Eberechi Eze, mai shekara 25, sai dai suna fuskantar gogaya daga Manchester City kan dan wasan gefe na Ingila . (Football Insider)

Napoli na zawarcin dan wasa mai tsaron bayan Tottenham da Romania Radu Dragusin, wanda ya zo Ingila a watan Janairun da ya gabata sai dai Spurs ta na son a biyata yuro miliyan 40 a kan dan wasan mai shekara 22. (Sun)

Barcelona da Atletico Madrid sun rasa dan wasa mai kai hari na Ingila Mason Greenwood, dan shekara 22, inda Manchester United ta sanya fam miliyan 51.7 a kansa . (Marca - in Spanish)

Manchester United za ta sake zawarcin dan wasan tsakiya na Barcelona Frenkie de Jong, mai shekara 26, bayan ta kasa cimma matsaya da dan wasan Netherlands a shekarar 2022. (Mundo Deportivo - in Spanish).

Watakila mataimakin kociyan Manchester United Steve McClaren ya ci gaba da aiki a kungiyar har kaka mai zuwa ko da an kori kocin kungiyar Erik ten Hag daga mukaminsa da sauran tawagarsa (Mirror)

Kokarin da Arsenal ke yi wajan daukar dan wasan tsakiya na Sfaniya Martin Zubimendi ya gamu da cikas bayan da kocin Real Sociedad Imanol Alguacil ya ce ba za a sayar da dan wasan mai shekara 25 a wannan bazara ba . (Metro)

Arsenal za ta cefanar da ‘ yan wasanta su 7 ciki har da masu bugawa Ingila wasa su uku da suka hada da Aaron Ramsdale mai tsaron raga mai shekara 25 da Eddie Nketiah mai kai hari dan shekara 24 da dan wasa tsakiya Emile Smith Rowe, mai shekara 23. (Mirror)

Watakila dan wasan tsakiya na Jamus Pascal Gross mai shekara , 32, ya bar Brighton zuwa Eintracht Frankfurt a wannan bazara (Florian Plettenberg)

Everton na son dan wasa mai kai hari na Leicester City da Nijeriya Kelechi Iheanacho, dan shekara 27. (Football Insider)

Bayern Munich na zawarcin kocin Crystal Palace Oliver Glasner a matsayin wanda zai maye gurbin Thomas Tuchel sai dai dan kasar Austria mai shekara , 49, na son ya ci gaba da zama a Selhurst Park. (Sky Sports)

Real Madrid za ta jira sai bayan wasan karshe na gasar zakarun turai da za ta buga da Borussia Dortmund a ranar 1 ga watan Yuni kafin ta sanar da daukar dan wasa mai kai hari na PSG da Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 25 (Athletic - subscription)