Chelsea na fafutar neman gurbin shiga gasar Turai ta badi

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea na neman gurbin shiga gasar kofin zakarun Turai ta badi, bayan da ta je ta ci Nottingham Forest 3-2 ranar Asabar a gasar Premier League.

Minti takwas da fara wasa Chelsea ta ci kwallo ta hannun Mykhaylo Mudryk, sai dai minti takwas tsakani Forest mai masaukin baki ta farke ta hannun Willy Boly.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Forest ta kara na biyu ta hanun Callum Hudson-Odoi, amma minti shida tsakani Raheem Sterling ya farke.

Saura minti takwas a tashi daga karawar Nicolas Jackson ya zura na uku a raga da hakan ya bai wa Chelsea maki ukun da take bukata.

Da wannan sakamakon Chelsea tana nan a matakinta na bakwai da maki 57, iri daya da na Newcastle United ta shida.

Ita kuwa Forest tana ta 17 da tazarar maki uku tsakaninta da Luton ta ukun karshen teburi, kuma saura wasa daya da kowacce za ta buga ranar Lahadi 19 ga watan Mayu.

Chelsea tana da wasa biyu da za ta kara da ya hada da na Brighton da za ta kai ziyara da kuma Bournemouth da za ta buga a Stamford Bridge ranar 19 ga watan Mayu.

Manchester United ce ta takwas din teburi da tazarar maki uku tsakani da Chelsea ta bakwai da kuma Newcastle United ta shida.