Rodri ya yi wasa 48 a jere ba a ci Man City ba a Premier League

Rodri

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City ta doke Fulham 4-0 a wasan mako na 37 a Premier League ranar Asabar, kenan ta koma ta daya a kan teburin kakar bana.

Rodri ya buga mata wasan, kuma na 48 kenan a jere a Premier League, na 71 jimilla da ba a doke Manchester City ba.

Rabon da a ci City tare da Rodri a cikin fili a Premier League tun cikin Fabrairu, bayan da Tottenham ta yi nasara 1-0.

A wasannin da City ta buga da Rodri a cikin fili ta ci 39 da canjaras tara a fafatawa 48 a jere a babbar gasar tamaula ta Ingila ba tare da rashin nasara ba.

A tarihin gasar Premier League Sol Campbell ne ya yi wasa 56 a jere ba tare da rashin nasara ba a Arsenal tsakanin Nuwambar 2002 zuwa Oktoban 2004.

Bayan da City ta ci Fulham ya sa tata koma ta daya a kan teburi da maki 85 da tazarar maki biyu tsakani da Arsenal ta biyu.

Ranar Lahadi Arsenal za ta je Manchester United a Old Trafford, domin buga wasan mako na 37 a Premier League.

City mai fatan kafa tarihin lashe Premier na hudu a jere za ta kara da Tottenham ranar Talata a Landan daga nan ta karbi bakuncin West Ham a ranar karshe.

Za a kammala wasannin karshe a Premier League ta bana ranar Lahadi 19 ga watan Mayu.