Man City ta kusan daukar Premier League na bana

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta koma ta daya a kan teburin Premier League, bayan da ta doke Fulham 4-0 a Craven Cottage ranar Asabar.
Josko Gvardiol ne ya ci kwallo biyu da hakan ya sa matsi ya hau kan Arsenal, wadda ta koma ta biyu a teburin Premier da tazarar maki biyu.
City ce ta mamaye karawar tun daga farko har zuwa tashi daga wasan, inda Gvardiol ya fara cin kwallo.
Phil Foden, wanda ke kan ganiya ne ya ci na biyu, bayan da suka koma zagaye na biyu a wasan na mako na 37 a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Kadan ya rage Erling Haaland ya kara na uku, amma sai dan wasan ya buga kwallo ta yi sama ta fita waje.
Daga nan ne City ba ta jira ba ta kara na biyu ta hannun Gvardiol, kuma na biyu da ya zura a raga a wasan.
An bai wa Issa Diop jan kati daf da za a tashi wasan, bayan da ya yi wa Julian Alvarez keta, wanda shi ne ya buga fenaritin ya kuma ci kwallon.
Da wannan sakamakon Arsenal na bukatar doke Manchester United ranar Lahadi, idan ya so ranar wasan karshe a fayyace wadda za ta dauki kofin bana.
Manchester City za ta kara da Tottenham ranar Lahadi, idan Arsenal ta kasa samun sakamako mai kyau a Old Trafford, kenan City ta lashe Premier na hudu a jere.

Asalin hoton, BBC Sport










