Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda 'yan adawa ke tururuwar komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
Yadda jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ke ci gaba da samun karuwar mabiya daga jam'iyyun hamayya, wani abu ne da ke jan hankali a kasar.
Kusan 'yan majalisar tarayya da dama a Najeriyar ne suka sauya sheka zuwa APC.
A baya-bayannan ma dai wasu manyan 'yan siyasa daga jam'iyyun hamayya a jihar Kaduna da suka hada da PDP da NNPP sun koma jam'iyyar APC.
Sakataren jam'iyyar APC na kasa Malam Bala Ibrahim, ya ce gaskiya ce ke yin halinta.
Malam Bala Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa, "Ga masu cewa muna fatan da matsaloli da rigingimu, ai yanzu suna jin kunya, kuma akwai wasu daga cikinsu ma har sun dawo jam'iyyarmu ta APC."
"Wannan dai na ba wani abu bane face nuni da cewa manufofin jam'iyyar APC manufofi ne na gari wadanda suka zo dai-dai da dimokradiyya. Sanna ga adalci da tsari da ake bukata a dimokradiyya," in ji shi.
Wasu da suka koma jam'iyyar APC daga jam'iyyun adawar sun ce rikice-rikicen da ake fama da su a jam;iyyarsu ne ya sanya su sauya sheka.
Sai dai kuma Umar Ibrahim Tsauri, mamba a kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, ya shaida wa BBC cewa rashin akida ce ke sanya wasu sauya sheka.
Ya ce " Mafi yawan mutanen da ke sauya sheka musamman a yanzu ba mamaki ko dai sun nemi wani abu a jam'iyyar da suke basu samu ba, ko kuma suna hangen cewa a adawa ba a samun komai gara su koma jam'iyya mai mulki."
Ya ce "Idan ba wadannan dalilai ba, to ba mamaki mutum ya yi wani laifi ne yana tsoron za a iya kai wa gareshi, to sai ya bar jam'iyyarsa ta asali ya koma jam'iyyar APC domin laifin da ka aikata a jam'iyyarka ta baya ya wuce kawai."
Sauya shekar 'yan siyasa dai abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya.
Masana kimiyyar siyasa a Najeriya dai sun ce 'yan siyasar kasar basu gaji azumin siyasa ba.
Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin kimiyyar siyasa ne a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, a siyasar Najeriya ana cewa 'yan siyasar ba sa maraici, ma'ana idan suna jam'iyya sai tazo bata ci zabe ba, to sai su tashi su koma jam'iyya mai mulki.
Ya ce "Irin wannan abun na kawowa jam'iyya matsala, domin a wani lokaci sai kaga ana rigin-rigimu a tsakanin 'yan jam'iyyar na ainihi da kuma baki wadanda suka sauya shekara suka koma cikinta, musamman akan abin da ya shafi rabon mukami da bayar da kwangiloli."
Salon sauya shekar dai na tasiri wajen karawa jam'iyya mai mulki karfi.