Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin Peter Obi na son kwance wa masu yunƙurin haɗewa zane a kasuwa ne?
A daidai lokacin da wasu ke hanƙoron ganin jam'iyyun adawa a Najeriya sun haɗe domin kafa jam'iyya mai ƙarfi da za ta ƙalubalanci jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen shekarar 2027, da alama akwai jan aiki a gaba.
Ɗaya daga cikin waɗanda ake tunanin yana cikin na gaba-gaba wajen haɗakar, wato tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a Jam'iyyar Labour, Peter Obi, wanda ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi na 2023 ne ya fara nuna kamar zai yi tutsu, inda ya nesanta kansa daga duk wani yunƙurin da ake yi na haɗakar a yanzu.
Ya ce shi ba ya cikin wannan batun, yana mai cewa shi yanzu babban abin da ke gaban shi su ne magance matsalolin da suke fuskantar Najeriya, kamar talauci da rashin tsaro.
Obi ya bayyana haka ne a wani taron da aka yi a Abuja domin ƙarfafa dimokuraɗiyya, wanda cibiyar nazarin dimokuraɗiyya da siyasa wato Centre for Democracy and Development (CDD) da cibiyar nazarin shugabanci ta Afirka wato African Centre for Leadership, Strategy and Development LSD da sauransu suka shirya.
Obi ya soki yadda wasu suka fi fifita harkokin siyasa, sama da tattauna hanyoyin magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta, sannan ya buƙaci a ƙara ƙaimi wajen tabbatar da jin daɗin ƴan ƙasar.
Ya ce, "ba na sha'awar duk wata tattaunawa a yanzu da za a yi kan karɓe mulki a zaɓen gaba. Kamata ya yi a yi maganar Najeriya. Yaya za mu samar da tsaro? yaya za mu inganta rayuwar talaka? yaya za a inganta ilimin yaranmu. Waɗannan su ne suka fi muhammanci a yanzu," kamar yadda aka ruwaito shi yana faɗa a tattaunawarsa da manema labarai bayan taron.
Akwai buƙatar jam'iyyun adawa su haɗu - Atiku, El-Rufai
Obi ya yi waɗannan kalaman ne bayan taron, wanda tsohon ɗantakarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana buƙatar da ke akwai na jam'iyyun hamayya su haɗe, inda ya yi zargin cewa jam'iyyar mai mulki na cigaba da yun yunƙurin haɗiye jam'iyyun adawa a ƙasar domin hana su rawar hantsi.
A wurin taron, an tambayi Atiku Abubakar ra'ayinsa kan zargin ci-da-ƙarfi da jam'iyyu masu mulki ke yi a Najeriya, inda ya ce, "kamar yadda El-Rufai ya faɗa ne, ya kamata jam'iyyun adawa su yi tunanin abin da ya dace domin magance wannan matsalar, domin idan ba haka, za mu wayi gari, mun kashe dimokuraɗiyya," in ji shi.
Atiku ya ƙara da cewa wataƙila tarihi ne zai maimaita kansa, "domin irin wannan barazanar ce ta sa aka assasa APC. Ya kamata mu riƙa ɗaukar darasi daga tahiri."
Shi ma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce, "yadda ake yunƙurin haɗiye jam'iyyun adawa babbar matsala ce da ta kamata ta ɗaga hankalin kowa."
Ya ce akwai wata ƙididdiga da ta nuna cewa kusan kashi 75 na ƴan Najeriya masu katin zaɓe ba sa tunanin kaɗa ƙuri'a a zaɓen 2027, inda ya ce, "wannan babbar matsala ce, don haka nake tunanin dole kowa ya tashi tsaye domin fafutikar tabbatar da dimokuraɗiyya."
"Mu da muka kai shekara 60, mun san mulkin soja, kuma ba ma son mulkin soja, amma kuma ba ma son fararen hula suna mulki irin na soja,"
El-Rufai ya ce akwai waɗanda ake dasawa a jam'iyyu hamayya, domin hana su zaman lafiya.
An dai daɗe ana zargin jam'iyyar APC da kitsa rikice-rikice a jam'iyyun adawa domin hana su sakat, zargin da ta daɗe musantawa.