Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
APC na son rufe bakin ƴan adawa - Atiku
A Najeriya jam'iyyun hamayya na ci gaba da bayyana jam'iyyar APC mai mulki a matsayin mai mulkin kama karya.
Na baya-bayan nan shi ne tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar hamayya ta PDP, Atiku Abubakar, shi ma ya zargi APC da amfani da karfi da barazana wajen neman hana 'yan hamayya 'yancin fadin albarkacin baki.
Atiku na mayar da martani ne game da kalaman da sakataren watsa labaran jam'iyyar APC, Felix Morka ya yi a kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, kan salon mulkin APC, inda Mista Felix ya yi wa Obi kashedi a kan tsokacin da yake game da tafiyar mulkin shugaban Najeriyar, Bola Ahmed Tinubu.
Atiku Abubakar ya ce akwai matakai da dama da gwamnatin Najeriyar ke dauka na murkushe 'yan adawa, kuma kamata ya yi su nemi afuwar Peter Obi da ma 'yan Najeriya kan halin da kasa ke ciki.
Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Abdurrashid Uba Sharada, ya shaida wa BBC cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowanne dan kasa dama da 'yancin fadin albarkacin bakinsa da tsokaci kan abin da suke ganin ya shafe su.
Ya ce : ''Kalaman Atiku kamar mataki ne na zaburar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, da tunatar da su cewa mulkin dimukuradiyya muke yi, idan har kalamai irin haka za su dinga dauka to kuwa hakan babbar barazana ce da ci gaban dimukuradiyyar kasarmu.''
''Hakan na nuna cewa an fara komawa kan tsarin mulkin kama karya, don sun fito sun karyata maganganun da sakataren watsa labaran - Felix Morka ya yi hakan ba yana nufin shikenan ba, ai su ba ai musu haka ba a lokacin suna 'yan adawa, an ba su damar cin gashin kai kamar yadda dimukuradiyya ta ba su dama, don haka wannan salon da suka fito da shi na razanar da 'yan adawa ba zai yi tasiri ba, ba kuma za mu zuba ido haka nan ba,'' in ji Aburrashid Shehu.
Sai dai jam'iyyar APC ta yi martani ga jam'iyyun hamayyar, Malam Bala Muhammad shi ne mai magana da yawun APCn inda ya ce suna mamakin yadda jam'iyyun adawa ke juya magana da jirkita ma'anar abin da sakataren watsa labaran ya yi.
Ya ce ya kamata 'yan adawar su kara kwarewa wajen sanin makamar aiki, da sanin mulkin dimukuradiyya.
''Ba zagi ko barazana ce ba, kamar abin nan da Shata ke cewa idan ka ji an ce mutum aniyarsa ta bishi, to daman aniyar tashi ce ba ta da alkhairi tun farko shi ya sa suke jin tsoro kuma suka firgita, don haka ba za su iya ba.''
Kan batun matsin da 'yan kasa ke ciki da batun karin haraji da gwamnatin Tinubu ke yi, wanda na daga cikin abin da 'yan adawa ke taya 'yan Najeriya kokawa, Bala Ibrahim ya ce shi ma shugaban kasa ya san da hakan, amma mataki ne da nan gaba 'yan Najeriya za su yi alfahari da shi.
''Da sun saurari jawabin shugaban kasa, ya amsa cewa ana jin jiki, shi ma yana jin jikin ba zai yiwu a shasshafa kashin wanda aka karya haka nan ba, dole sai an dauki matakan da zai ji ciwo da jin zafi. Amma daga baya idan ya samu sauki zai ji dadi,'' in ji Bala Ibrahim.
'Yan Najeriya dai na ci gaba da kokawa kan halin da kasa ke ciki na tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi da na bukatun yau da kullum.
Hakan ya biyo bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki a shekarar 2023.