Me ya sa ake musayar yawu tsakanin APC da PDP?

Lokacin karatu: Minti 2

Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin babban zaɓen Najeriya na 2027, ana ci gaba da musayar yawu kan shirye-shiryen manyan ƴansiyasa da ke hamayya da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda suke tarurruka tare da tuntuɓar juna kan yadda za su kayar da jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2027.

Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da martani kan kalaman da wasu daga cikin ƴaƴan jam'iyyun adawa da waɗanda suke na cikin gidanta suka yi, inda suka zarge ta da sauka daga kan turba.

Fadar shugaban na mayar da martani ne bayan wani taro da jagororin hamayya da Jam'iyyar ta APC da wasu daga cikin ƴaƴanta da ke adawa da gwamnatin suka gudanar a Abuja.

Jam'iyyar ta APC dai ta ce hakan ba komai ba ne illa yunƙurin da masu adawa da gwamnatin ta Bola Ahmed Tinubu ke yi na kawar da hankalin Tinubu daga hidimta wa ƴan Najeriya.

Sai dai jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriyar ta ce, borin kunya gwamnatin APC ke yi, saboda manuniya ta nuna cewar ƴan Najeriya sun gaji da mulkinta.

Abdul'azizi Abdul'aziz ɗaya ne daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriya ya kuma ce ganin irin rawar da shugaban na Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke takawa wajen gyara kura-kuran da jam'iyyar PDP ta yi a Najeriya, tsawon shekaru 16 da suka ɗauka suna mulki ne yasa suke kaɗa gangar siyasa tun kafin lokacin yazo.

"Su waɗanda suke waɗannan zarge-zargen ai sune mutanen da suke ɗauke hankalin gwamnati daga kan abin da ya kamata." In ji Abdul'aziz.

Mataimakin mai magana da yawun jam'iyyar PDP a Najeriya, Ibrahim Abdullahi, ya ce martanin fadar shugaban ba komai ba ne illa shure-shure da baya hana mutuwa.

"Wanda duk ya iske shinkafa naira 6,000 da PDP ta faɗi zaɓe, yanzu ya sayi shinkafar nan kan naira 100,000, lallai kam ana gyara." a cewar Ibrahim.

Fadar shugaban Najeriya ta ce taron da suka gudanar ba komai ba ne illa na waɗanda ba sa fatan ci gaban Najeriya, da yaɗa tunzuri, da barazana da, ra'ayoyin da za su durƙusar da dimokaraɗiyya.

Jam'iyyun hamayya a Najeriya na fama da rikice-rikicen cikin gida, lamarin da masana kan harkokin siyasa ke bayyanawa da ka iya kawo tarnaƙi wajen haɗewar tasu.

A shekarar 2023 ne dai Shugaba Bola Tinubu ya yi nasarar doke Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa, inda aka samu wasu gwamnonin PDP da ake zargin sun yi wa APC aiki.

Yanzu dai hankali ya karkata ne ga kallon irin wainar da za a toya a tandar babban taron jam'iyyar PDP, wadda ke kan gaba a sahun jam'iyyun hamayya a Najeriya.