Mene ne babban layin wutar lantarki na Najeriya da ke lalacewa?

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Larabar 10 ga watan Satumbar 2025 ne babban layin wutar lantarkin Najeriya sake lalacewa a karo na farko a shekarar.

Duk da cewa babu cikakkun alƙaluma dangane da yawan lokacin da babban layin wutar lantarkin na Najeriya ya lalace, bayanai sun nuna cewa ya lalace sau fiye da 100 a tsawon shekaru 10 sannan sau 12 a shekarar 2024.

Bayanin da kamfanin wutar lantarki na Abuja, AEDC ya wallafa a shafinsa na X ya nuna cewa wutar ta faɗi daga megawatts kusan 3000 a ƙasar zuwa megawatts 1.5 a ranar Larabar.

Shin mene ne wannan babban layin wutar lantarki, kuma me ya sa yake yawan lalacewa?

Yaya babban layin lantarkin yake?

..

Asalin hoton, Getty Images

Babban layin wutar lantarki na Najeriya ko kuma "National Power grid" a Turance - gungun layuka ne da suka haɗa tashoshin samar da lantarki da ke bai wa dukkan sassan Najeriya wuta.

A taƙaice, wata ma'dana ce da ke ɗauke da dukkan lantarkin da ake sha a Najeriya. Haka nan, ba wani wuri ba ne guda ɗaya, tarin layuka ne a wurare daban-daban.

An tsara shi ne don ya yi aiki ta wasu taƙaitattun hanyoyi musamman dangane da yawan wutar da ake da ita, da tsaron lafiyarsa.

Saboda haka duk sanda ya fita daga yanayin da ya saba zama na kwanciyar hankali, ayyukan da yake za su samu matsala kuma hakan kan sa ya lalace.

Na'urorin da ke ba da wutar lantarkin kan kashe kansu da zarar sun fuskanci cewa suna cikin matsala.

Hakan ka iya nufin ɗaukewar wutar gaba ɗaya ko kuma na wani ɓangare.

Kazalika, yanayi - iska ko ruwa ko sanyi ko zafi - kan shafi aikin babban layin a wasu lokuta, abin da ya sa ke nan ake yawan ɗauke wuta idan aka fara iska mai ƙarfi a lokuta da dama.

Me ke sa lalacewar babban layin?

Injiniya Muhammad Sade shugaban kamfani mai zaman kansa na samar da wutar lantarki a Najeriya na Power Africa Energy, lalacewar babban layin na nufin ɗaukewar wuta a ƙasa baki ɗaya, yayin da kuma samun tangarɗar layin ke nufin rasa wuta a wasu ɓangarori na ƙasa.

Injiniya Muhammad Sade shugaban kamfani mai zaman kansa na samar da wutar lantarki a Najeriya na Power Africa Energy ya ce dalilin da ke sa babban layin wutar lantarki na Najeriya ke lalacewa shi ne tsufan da kayan samar da wutan suka yi.

"Tun daga injinan da ke samar da wutar zuwa masu rarraba ta dukkan su sun riga sun tsufa. Sannan kuma yawan ƴan Najeriya da yawan wutar da suke buƙata sun fi ƙarfin injinan waɗanda tsofaffi ne." In ji Injiniya Muhammad.

Hanyoyi huɗu na magance matsalar lalacewar

..

Asalin hoton, Getty Images

Wata majiya a kamfanin TCN ta shaida wa BBC cewa lalacewar babban layin ba abu ne da ke buƙatar gyara ba idan hakan ta faru, sai dai a sake kunna layin wato mayar da shi bakin aiki.

To sai dai kuma injiniya Muhammad Sade ya ce duk wani abu da za a yi wa babban layin zai zama na wucingadi kasancewar injinansa sun tsufa, inda ya lissafa hanyoyin gujewa

  • Sabunta injina: Dole ne a sabunta injinan babban layin nan kamar yadda a baya gwamnati ta yi ƙoƙarin sabuntawa ta hanyar shiga yarjejeniya da kamfanin Siemens.
  • Sa ido kan babban layin: Dole ne a koyaushe a rinƙa sanya idanu kan babban layin wutar.
  • Kula da hawa da saukar wuta: Ya kamata a rinƙa kula da hawa da saukar wutar da babban layin yake sarrafawa. Misali idan wuta na 50Hz ta dawo 45 to za a iya samun lalacewar layin.
  • Ƙara yawan babban layi: A wasu ƙasashen a kan samu manyan layukan samar da wutar ne ta yadda idan wannan ya lalace to za a koma kan ɗayan. Sannan dole ne a rinƙa amfani da hanyoyin samun wuta da suka haɗa da hasken rana.