...Daga Bakin Mai Ita tare da Shettima Mansur Ahmad
...Daga Bakin Mai Ita tare da Shettima Mansur Ahmad
A shirinmu na ....Daga Bakin Mai Ita na wannan mako mun kawo muku tattaunawa da Muhammad Ahmad Tijjani da aka fi sani da Mansur ko Shettima bayan samun sarauta daga Shehun Borno.
An haife shi a shekarar 1965, kuma ya fara waa kusan shekara 38 da suka wuce, kamar yadda ya bayyana wa BBC.
Ya ce ya fara waƙa ne sakamakon yawaitar sauraron waƙoƙi a gidan radiyo da ake yawan kunnawa a gidansu.
Mawaƙin ya yi waƙoƙi masu yawa, sai dai ya ce waƙar da ya yi kishin ƙasa mai taken Najeriya Uwa ɗaya Uba ɗaya ce bakandamiyarsa.
Kafin ya fara waƙa ya yi sana'o'i da yawa ciki har da yaron mota.



