Wane tasiri 'rundunar tsaron lantarki' za ta yi ga tsaron tasoshi da turakun wutar a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta kafa wata runduna ta musamman da za ta yi aikin kare layuka da cibiyoyin samar da wutar lantarkin ƙasar daga bata-garin da ke kai musu hari suna lalata su.
Ministan cikin gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a Juma'a a wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce jami'an da za a samar za su fito ne daga jahohin ƙasar 36 kuma za su samar da cikakken tsaron da zai kawo ƙarshen katsewar layukan da ke yawan samu a ƙasar.
Katsewar wutar lantarki a Najeriya kusan ya zama ruwan dare, abin da kuma ke ci gaba da ke durƙusar da sana'o'in jama'a da sauran ɓangarorin kiwon lafiya da ma walwalar jama'a.
Wane tasiri tsarin zai yi?
Masana tsaro na yi wa tsarin kallon wani abun da ya kamata a yi tuntuni ba wai yanzu.
"Duk wani tsari da aka kawo domin warware matsala to lallai abu ne mai kyau kuma abin a yaba ne. Akwai wuraren daɓata-gari ne ke kai hare-hare domin su sace dalmomi da ƙarafa da wayoyin da ake amfani da su a waɗannan tashoshi da ake amfani da su. Ka ga a irin wannan wurin tsarin da minista ya yi bayani zai yi aiki na kai jami'an civil defence su bayar da kariya." In ji Barista Audu Bulama Bukarti fitaccen lauya kuma mai bincike kan sha'anin tsaro a yankin Sahel.
Masanin tsaron ya ce wasu wuraren da ake sace kayan lantarkin yankuna ne da 'yan bindiga ke da sansanoni, abin da samar da jami'an tsaron da suka dace da kowane wuri zai fi dacewa.
"Akwai wasu jihohin da ƴanta'adda da ƴan bindiga ne ke kai hare-hare kan irin waɗannan tashoshi kuma mun san cewa ƴansanda ma sun kasa samar da tsaron nan ballantana civil defence."
"A yi tsari da idan ana buƙatar ƴansanda sai a kai su. Wurin da ya kamata a kai jami'an civil defence sai akai su. Akwai buƙatar isassun bayanai da kayan aiki sosai wataƙila ma har da jirage da jirage marasa matuƙa domin tattara bayanai da kuma isa wurin a kan lokaci idan an samu bayanai lokacin da aka samu matsala."
"Domin kuwa hanya ɗaya tilo ta maganin matsalar tsaro shi ne a kai wa waɗannan mahara ko ƴanta'adda yaƙi har maɓoyarsu." In ji Bulama Bukarti.
Me ke janyo hare-hare kan muhimman wurare?

Asalin hoton, TCN
Barista Bulama Bukarti ya ƙara da cewa duk da dai ƴanta'adda da ƴanbindiga na kai hare-hare muhimman wurare da manufar yi wa ƙasa zagon ƙasa, amma ya alaƙanta talauci da ɗaya daga cikin dalilan da ke janyo irin waɗannan hare-hare.
"Sai gwamnati ta sassauta manufofinta da suka janyo talauci a tsakanin ƴan ƙasa saboda laifuka kan ƙaru sakamakon yawaitar yunwa da fatara ciki har da kai hare-hare a wurare da ake gani suna da abubuwa masu muhimmancin da za a iya sayarwa domin samun kuɗi." In ji Bulama Bukarti.
Matsalar wuta a Najeriya
A baya-bayan nan ana yawan samun tangarɗa na yawan katsewar wutar lantarki, a bisa dalilan da hukumomin Najeriya suka ta'allaka da sace wayoyi da sauran na'urorin samar da wutar da ɓarayi da sauran ɓata-gari ke yi ne.
Ko a watan Oktoban shekarar 2024 sai da wannan matsala ta katsewar layukan ta shafi yankin arewacin ƙasar gaba ɗaya, inda akalla jihohi tara na arewacin ƙasar suka kwashe kwana tara suna fama da rashin wutar lamarin da ya jefa harkokin rayuwa da na tattalin arziƙi cikin yanayi maras dadi.
Asibitoci da masana'antu da gidajen al'umma duka sun faɗa cikin wani hali, inda sakamakon rashin wutar a asibitoci ke jawo jama'a na rasa rayukansu,a cewar rahotonni, sannan gidaje na fuskantar matsalar rashin ruwan sha.
Katsewar lantarki a yankin na arewa na zuwa ne ƴan kwanaki bayan ɗaukacin ƙasar ta yi fama da katsewar wutar har sau uku a cikin kwana biyu sakamakon lalacewar babban layin wutar na ƙasa wato national grid.











