Waɗanne illoli amfani da bam kan cibiyoyin nukiliyar Iran zai haifar?

Asalin hoton, Getty Images / Maxar Technologies.
- Marubuci, Rebecca Morelle, Alison Francis and Victoria Gill
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Science Team
- Lokacin karatu: Minti 4
Isra'ila tana ta kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran hare-hare, inda take son kai wa ga cibiyoyin sarrafa sinadarin uranium da ke ƙarƙashin ƙasa.
Cibiyar nukiliyar ta Iran da ke Natanz a tsakiyar ƙasar ta samu matsala sakamakon hare-haren kamar yadda hukumar sa-ido kan makaman nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, IAEA ta ce.
Fordo wadda ita ma cibiyar nukiliyar ta Iran ce wadda kuma ke can cikin duwatsu a ƙarƙashin ƙasa. Cimma wannan cibiya na buƙatar bama-bamai masu dogon zango a ƙarƙashin ƙasa kuma Amurka ce kawai ta mallake su.
To ko mene ne hatsarin da ke tattare da amfani da bam wajen lalata cibiyar ta Fordo?
Hukumar IAEA dai ta ce hare-haren kan nukiliyar Iran "abin takaici" ne.
A ranar Litinin, Darekta Janar na hukumar ta IAEA, Rafael Grossi ya ce "yaƙin na ƙara yawan hatsarin fallatsar tururin sinadaran nukiliyar da zai cutar da al'umma da muhalli."
Ana dai amfani da cibiyoyin sarrafa sinadarin uranium ne wajen samar da wani nau'i na sinadarin ko kuma nau'in da ake kira isotope na uranium ɗin.
"Lokacin da aka haƙo sinadarin uranium daga ƙasa, yana fitowa a nau'i guda biyu: kaso 99.3 kan zama uranium samfirin 238 sannan kuma kaso 0.7 kan zama uranimu nau'in 235 kuma wannan ne ake buƙatar a na'urorin sarrafa sinadarin zuwa nukiliya." In ji Farfesa Paddy Regan na jami'ar Surrey da ke Burtaniya.
Fallatsar makamashi
Tsarin bunƙasa nukiliya shi ne ƙara yawan sinadarin uranium-235.
Ana yin hakan ne ta hanyar tsame sinadarin na uranium daga asalin yadda yake a iska sai a dama ta hanyar sarrafa shi da na'urar da ake kira centrifuges, kamar yadda Frafesa Regan ya ce.
Kuma saboda uranimu-238 ya fi uranium-235 nauyi sai wannan nau'urar sai ta tace ta raba nau'in sinadaran guda biyu. Za a yi ta damawa da markaɗa su har a cimma abin da ake so.
Tashoshin wutar lantarki nanukiliya kuma na buƙatar kimanin kaso 3-5 na sarrafaffen uranium da za su samar da ƙarfin nukiliyar da zai fitar da makamashi.
To amma idan buƙatar ita ce samar da makamin nukiliya, za a buƙaci kaso mai yawa na sinadarin uranium-235 -kusan kaso 90 na sinadarin.
Daidai yawan sarrafa sinadarin da bunƙsa shi daidai girman makamashin da zai saki.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hukumar IAEA ta ce bunƙasar uranium da ƙasar Iran ke yi ya kusan kaso 60 wadda hakan ke nufin ana dab da cimma makamin nukiliya.
To amma harba makamin roka zuwa cikin rumbun sinadarin ba zai haifar da "matsalar nukiliya" ba wanda zai daidai da hatsarin da aka fuskanta a cibiyoyin sarrafa makamashin nukiliya na Fukushima ko Chernobyl.
"Sinadarin uranium ɗin da aka sarrafa shi sosai na ɗauke da tururin guba fiye da wanda ba a sarrafa ba kusan ninki uku. Sai dai kuma gubar da ke cikin dukkannin ba mai yawa ce sosai ba. Gubar ba za ta yi wa muhalli illa mai yawa ba," in ji Farfesa Jim Smith na jami'ar Portsmouth wanda kuma ya yi nazari dangane da sakamakon bala'in fashewar cibiyar nukiliya ta Chernobyl.
"Mun fi damuwa da abin da ake kira da warwatsuwar sinadarin - yadda sinadarin ke warwatsuwa idan yana cikin na'urar sarrafawa ko kuma yana ƙunshe a cikin bam - suna ɗauke da abubuwa kamar gubar caesium da ta strontium da nau'in iodine. Su ne suke gurɓata muhalli."
To amma sakamakon yanzu ana sarrafa sinadarin a cibiyoyin - fashewar bam ba za ta haddasa hatsari ba tunda babu warwatuswar sinadarin, in ji shi.
Za dai a iya warwatsa sinadarin na uranium ta hanyar tarwatsa shi a gargajiyance.
Illa ga mazauna kusa da cibiyoyin nukiliya
Hukumar IAEA ta samu guba a cibiyar nukiliya ta Natanz bayan hare-haren bama-bamai, amma kuma ta ce gubar ba za ta cutar ba.
"Gubar uranium ba ta yin nisa sosai," in ji Farfesa Claire Corkhill, shugabar sashen binciken albarkatun ƙasa da gubarsu a jami'ar Bristol.
To amma ga mutanen da ke kusa da cibiyar, za a iya samun matsaloli ga lafiyarsu, in ji ta.
"Dangane da abin da ya shafi guba ga jikin ɗan'adam, lallai babu wanda zai so ya shaƙi ɓuraguzan sinadarin uranium kuma ba wanda zai so ya ci su ko ya sha su," ta yi ƙarin haske.
"Saboda ɓuraguzan uranium ɗin ka iya zama a ƙwayoyin halittar mutum -ko dai cikin huhu ko ciki ta yadda gubar za ta rinƙa zagwanyewa har zuwa yanayin da za ta cutar da jiki."
Sannan kuma sakamakon tururun guba, hakan ka iya zama abu mai hatsari ga mutanen da ke kusa da wurin.
"Idan aka samu yanayin da na'urorin sarrafawa na centrifuges suka saki sinadarin uranium hexafluoride, tare da iskar gas ɗin da ke cikinsu to za a iya samun mummunan hatsari," in ji Farfesa Simon Middleburgh, masanin kimiyyar nukiliya a jami'ar Bangor.
"Idan wannan sinadarin na hexafluoride ya zo da iska mai tafe da damshi, to hakan na da babbar matsala saboda gubar da ke ciki," in ji shi.
"To amma ba zai haddasa mummunar matsala ga muhalli fiye ga mutanen da ke kewaye da cibiyar."
Hukumar IAEA ta ce sashinta mai kula da ayyukan gaggawa na aiki babu dare babu rana kuma yana ci gaba da sa ido kan yanayin da cibiyoyin nukiliyar Iran suke da kuma yawan tururin sinadarin uranium da ke cibiyoyin.











