Amsoshin tambayoyi takwas kan yaƙin Iran da Isra'ila

Asalin hoton, Getty Images
Isra'il da Iran na ci gaba da musayar wuta a tsakaninsu, yayin da Donald Trump ya ce sai nan da mako biyu ne zai yanke shawarar yiwuwar shigar Amurka cikin yakin ko akasin haka.
Ƙwararru a BBC da wakilanta sun masa wasu muhimman tambayoyi kan yaƙin daga masu bibiyarmu da masu yi a shafin intanet.
Me ya sa Isra'ila ke kai wa Iran hari a yanzu?
Isra'ila ta ɗauki matakin ne saboda ta yi imanin cewa Iran na dab da ƙera makamin nukiliya, kuma da alama tattaunawar da ake yi don hana ta ci gaba da shirin babu wani tasiri da yake yi, don haka wannan ce hanya ɗaya tilo da ta rage na dakatar da ita daga ƙudirin nata.
Ƙasar ta Isra'ila ta ce mallakar nukiliya ga Iran babbar barazana ce ga cigaba da wanzuwarta, ta ƙara da cewa idan har Iran ta mallaki makamin nukiliya za ta yi amfani da shi saboda a baya ta sha yin alwashin shafe ƙasar ta Isra'ila.
To sai dai ba lallai ne duka ƙasashen yankin sun yarda da wannan iƙirari na cewa Iran ta kusa mallakar nukiliya ba.
Kuma ba dole ne Hukumar Kula da Nukiliya ta Duniya ta Amince da hakan ba, haka kuma a rahoton baya-bayan nan da hukumar leƙen Asirin Amurka ta fitar, ba ta ambata cewa Iran ta kusa ƙera makamin nukiliya ba.
- Frank Gardner, Wakilin sashen tsaro na BBC
Ina fararen hular Iran ke tafiya?

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Isra'ila ta bayar da gargaɗin ficewa daga wasu yankuna a Tehran, babban birnin Iran, kuma galibin waɗannan unguwanni cike suke da mutane.
Mun riƙa ganin hotuna da bidiyon yadda wasu titunan birnin suka cika maƙil da ababen hawa da suka yi jerin gwano a ƙoƙarinsu na ficewa daga birnin zuwa wasu yankunan arewacin ƙasar, da suke ganin sun fi zaman lafiya.
To amma duk da haka an samu hare-hare a waɗannan unguwanni. Saboda hare-haren Isra'ilar na da yawa, babu wani yanki da ake ganin yana da tsaro.
Gwamnatin Iran ta ce za ta buɗe tasoshin jiragen ƙasa domin mutane su samu mafaka.
Birnin Tehran na da mazauna miliyan 10, don haka kwashe wanann adadi na mutane ba abu ne mai yiwuwa ba.
- Nafiseh Kohnavard, Wakiliyar BBC a yankin Gabas ta Tsakiya

Asalin hoton, Reuters
Idan Amurka ta shiga yaƙin, Iran za ta kai wa sansanoninta hari?

Asalin hoton, Getty Images
Akwai hatsarin hakan, amma abin da hakan zai janyo zai iya amfanar Amurkar.
Akwai dakarun Amurka kusan 40,000 zuwa 50,000 a wurare 19 a yankin Gabas ta Tsakiya. Akwai jami'an Amurka a Cyprus akwai kuma sansanin sojin ruwan Amurka a Bahrain.
Duka ya dogara da yadda Amurka ta yanke shawarar shiga yaƙin, da kuma lokacin da za ta ɗauka a yaƙin.
- Mikey Kay, mai gabatar da shirin tsaro na 'security Brief'
Shin ƙawayen Iran za su taya ta yaƙi da Isra'ila?
Ba na tunanin haka, hakan ba zai yiwu ba.
Tun bayan harin da Hamas ta kai wa Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023, Isra'ila ta gurgunta da dama cikin waɗanda za su iya kare Iran.
Sun kassara Hamas a Gaza, haka kuma sun murƙushe karfin Hezbllah a Lebanon, haka a Syria babu wata ƙungiyar kawar Iran tun bayan faɗuwar gwamnatin Bashar al-Assad, wanda babu hannun Isra'ila a ciki.
Haka ƙungiyar ƴantawayen Houthis na fama da rikici a Yemen. Don haka ƙarfinsu ba ya waje guda.
- Frank Gardner, wakilin sashen tsaro na BBC

Asalin hoton, EPA
Wane ne Jagoran addinin Iran, kuma wane goyon baya yake da shi?
Jagoran addinin Iran shi ne Ayatollah Ali Khamenei. Fitaccen malamin addini ne, amma yana da iko fiye da na shugaban Iran.
Shi ne babban hafsat hafsoshin tsaron ƙasar, kuma dole sai ya amince kafin yin kowane abu a ƙasar, ciki har da tattaunawa da Amurka kan shirin nukiliyarta.
To sai dai ba duka Iraniya ke goyon bayansa ba - Don haka akwai rarraubuwar kai kan goyon bayansa.
Shekaru biyu da suka gabata ƙasar ta fuskanci mummunar zanga-zangar adawa da gwamnati. Mata da dama sun fita zanga-zangar, suna buƙatar da a ba su ƴanci.
To amma duk da haka ba za mu kasa cewa gwamnatinsa na da farin jini tsakanin magoya bayansa ba, ciki har da rundunar sojin ƙasar mai alaƙa da gwamnatin.
- Nafiseh Kohnavard, Wakiliyar BBC a yankin Gabas ta Tsakiya

Asalin hoton, Reuters
Me zai faru idan aka kifar da gwamnatin Iran?
Babu tartibiyar amsa kan haka.
Cikin shekaru da dama da suka gabata mun sani cewa babu haɗin kai mai ƙarfi tsakanin ƴan hamayya da zai ba su damar kafa gwamnati.
Akwai zabi masu yawa, ciki har da Reza Pahlavi ɗan gidan tsohon Sha na Iran da a yanzu haka ke zaman gudun hijira a ƙasar waje.
Yana da magoya baya a cikin da wajen Iran, amma za mu iya cewa su ba su da yawa.
Yana da ƴan hamayya masu ra'ayin kawo sauyi a cikin gida, da ba za su so sake komawa mulkin sarauta ba da aka hamɓarar kusan shekara 40 da suka gabata.
Don haka babu tabbas ko za a samu sauyi a tsarin gwamnati.
- Nafiseh Kohnavard, Wakiliyar BBC a yankin Gabas ta Tsakiya
Ko Iran ta kusa mallakar makamain nukiliya?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mutanen da kawai za su iya tabbatar da hakan su ne amintattun masana nukiliya da ke aikin , da suka ƙunshin manƴan jami'an tsaron ƙasar da shi kansa jagoran addinin.
To sai dai a farkon watan ne aka samu ƙarin fargaba bayan da Hukumar Kula da Nukuliya ta Duniya, IAEA, ta samu Iran da laifin karya yarjejeniyar hana yaduwar nukiliya karon farko cikin kusan shekara 20, inda aka same ta da inganta sinadarin uranium zuwa kashi 60 cikin 100, kodayake bai kai matsayin ƙera makamin nukiyar ba.
A makon da ya gabata kuma sojojin Isra'ila suka ce ''bayanan sirri da suka samu a ƴan watannin baya-bayan nan sun nuna cewa Iran na dab da ƙera makamin nukiliya''.
To amma wane bayanan sirri?, domin ya saɓa binciken babbar ƙawarsu Amurka. A cikin watan Maris ne dakaktar hukumar tattara bayanan sirri ta Amurka, Tulsi Gabbard ta shaida wa majalisar dokokin Amurka cewa ''Duk da cewa Iran ta kai matsayin da ba ta taɓa kai wa ba wajen inganta snadaranta na uranium, har yanzu ba ta ƙera makamin nukiliya ba''.
A nata ɓangare, ita kuwa Iran ta sha nanata cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne.
- Frank Gardner, Wakilin sashen tsaro na BBC
Shin Isra'ila na da makamin Nukiliya?
Akwai ƙiyasin da ke nuna cewa tana da kusan makaman nukiliya 90. Amma a zahirin gaskiya ba mu san wannan amsar ba.
Ba ta taɓa tabbatarwa ko musanta mallakar makamin ba.
Isra'ila ba ta cikin ƙasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar daƙile yaɗuwar makaman nuiliya, wadda yarjejeniya ce da duniya ta amince da ita domin hana ƙasashe da yawa mallakar makamin.
Matakai uku ne ke sa a mallaki makamin nukiliya: Na farko ingantaccen ma'adinin uranium ya kai kashi 90 cikin 100, na biyu iya ƙera kan makamin, sai na uku yadda za a iya harba makamin inda ake so ya je.
Kawo yanzu Isra'ila ba ta bayyana cimma ɗaya daga cikin waɗanann matakai ba.
- Mikey Kay, mai gabatar da shirin tsaro na 'Security Brief' a BBC.











