Yadda ra'ayoyin ƙasashen Afirka suka bambanta kan yaƙin Iran da Isra'ila

Asalin hoton, Getty Images
Kafafen yaɗa labaru a Afirka sun wallafa martani mabambanta daga ƙasashen Afirka tun bayan ɓarkewar yaki tsakanin Isra'ila da Iran.
Kuma bayanan da suka fito daga gwamnatocin ƙasashen ya nuna yadda batun tattalin arziƙi da na diflomasiyya da kuma aƙida suka shafi matsayar da suka ɗauka.
Ƙasashe irin su Najeriya da Algeria da Afirka ta Kudu da Benin dukkanin su sun fito ƙarara sun yi tir da matakin da Isra'ila ta ɗauka na kai wa Iran hari, suna cewa hakan zai iya haifar da gagarumin rikici wanda illarsa ba zai misaltu ba.
Sai dai wasu ƙasashen kuma sun yi gum da bakunansu.
Rahoton jaridar Walf Quotidien ya ce "Ƙasashen Afirka da dama sun tsaya a tsakiya a kan yaƙin, wanda matakin ba zai rasa nasaba da muradan ƙasashen ba. Ƙasashen sun sani cewa ɗaukar ɓangare da ɗaya daga cikin ƙasashen biyu zai iya yin illa ga alaƙar diflomasiyya da ta tattalin arziƙinsu.
Kamar Isra'ila, ita ma Iran ta faɗaɗa alakar diflomasiyyarta da ta addini a ƙasashen Afirka da yawa," in ji jaridar.
Jaridar ta buga misali da ƙasashen da ke cikin sabon ƙawance na Sahel da Zimbabwe da Senegal da kuma Tanzaniya.
"Ita kuwa Morocco, ƙasa ce wadda take da alaƙa ta kut da kut da Isra'ila."
Saboda haka jaridar ta ce ƙasashe da dama na cikin halin gaba kura baya sayaki game da ƙasar da za su goyi baya, a saboda haka ne jaridar ta ce ƙasashe da dama sun gwammace su tsaya a tsakiya.
A ranar 13 ga watan Yuni Afirka ta Kudu ta yi kira da a kai zuciya nesa bayan Iran ta lashi takobin mayar da "zazzafan" martani kan hare-haren da Isra'ila ta kai mata.

Asalin hoton, EPA
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jaridar Malijet ta ƙasar Mali ta soki lamirin matakin da Isra'ila ta ɗaka na haramta wa kafafen yaɗa labarai ɗaukar rahotannin yaƙin a cikin ƙasar, inda ta bayyana matakin a matsayin "bakin-ganga", sannan ta buƙaci a mutunta ƴancin fadin albarkacin baki da kuma na al'umma.
"Me ya sa ake ƙyale wasu su yi abin da suke so wasu kuma a hana su? Sanya irin wannan takunkumi ga al'umma ba abu ne da za a amince da shi ba," in ji jaridar Malijet.
A ɓangare ɗaya, shugaban Benin Patrice Talon ya nuna damuwa kan "taɓarɓarewar matsalar tsaro cikin sauri a Gabas ta Tsakiya", kamar yadda jaridar 24Heures au Benin ta ruwaito.
Haka nan a Sudan jaridu sun ruwaito yadda rikicin Iran da Isra'ila zai iya ƙara haifar da sarƙaƙiya a yakin da ake fama da shi a Sudan.
Akwai rahotannin da ke cewa Iran na taimaka wa wani ɓangare na dakarun Sudan kai tsaye, duk da cewa gwamnatin Sudan ta musanta wasu daga cikin wadannan zarge-zarge da ake yi.
A ɓangare ɗaya Sudan da Isra'ila sun amince su daidaita alƙar da ke tsakaninsu a shekarar 2020, lamarin da ya sanya Amurka ta cire ƙasar daga jerin ƙasashen 'da ke taimaka wa ayyukan ta'addanci.'

Asalin hoton, Reuters
Jaridar Saudi Gazette a labarinta na 17 ga watan Yuni ta ruwaito ƙasashen Musulmai 20 waɗanda suka yi tir da matakin da Isra'ila ta ɗauka kan Iran.
A cikin ƙasashen 20, Masar da Chadi da Algeria da Djibouti da Sudan da Somaliya da Libiya da kuma Comoros duk ƙasashe ne na Afirka.
Labarin ya ce ƙasashen sun dauki matsayar ce ta hanyar wani sako da ƙasar Masar ta fitar, wanda ya samu sa hannun ministocin kasashen waje na ƙasashen.
Sauran ƙasashen su ne Saudiyya da Jordan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Pakistan da Bahrain da Brunei Darussalam da Turkiyya da Iraq da Oman da Qatar da kuma Kuwait.










