Mece ce IRGC, rundunar juyin-juya hali ta Iran kuma mene ne aikinta?

Dakarun Juyin juya halin Iran

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Rundunar IRGC na da rassa masu yawa da ke aiki ƙarƙashinta
Lokacin karatu: Minti 6

Yayin da yaƙi tsakanin Isra'ila da Iran ya shiga mako guda, dakarun rundunar juyin juya hali ta IRGC na ci gaba da ƙaddamar da hare-hare da yin amfani da samfuran makamai iri-iri.

Gidan talbijin na Iran ya ce sun kai hari kan tashar ruwan Isra'ila a Haifa da cibiyar tattara bayanan sirri ta Isra'ila da aka fi sani da 'Aman, baya ga cibiyar Mossad mai tattara bayanan sirri da cibiyar hada-hadar hannun jari ta Isra'ila da ke birnin Tel Aviv.

Hakan na zuwa ne bayan harin Isra'ila ya kashe shugaban sashen tattara bayanan sirri na dakarun juyin juya halin Iran, Mohammad Kazemi tare da mataimakinsa da wani babban jami'i, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Iran, IRNA ya bayyana a ranar Lahadi.

Shin me ce rundunar juyin juya halin Iran, da ake yawan ambatawa a baya-bayan nan?

Da gaske ne an kafa ta ne domin kare gwamnatin ƙasar da samar da daidaito tsakanin dakarun sojin ƙasar?

Kuma ta yaya aka faɗaɗa ayyukan rundunar zuwa kai hari ƙasashen waje?

Ƙarfin rundunar IRGC

Manjo Janar Mohammad Pakpour, babban kwamandan rundunar IRGC

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manjo Janar Mohammad Pakpour, babban kwamandan rundunar IRGC

Bayan faɗuwar gwamnatin Shah, sabbin hukumomin suka fara tunanin kafa wata runduna mai ƙarfi da za ta tabbatar da cimma muradun sabuwar gwamnati da kare ''muradunta na juyin juya hali.''

Daga nan ne manyan malaman ƙasar suka amince da kafa wata runduna mai ƙarfi da ta ƙunshi dakaru daga rundunar sojin ƙasar, mai haƙƙin kare kan iyakokin ƙasar da tsaron cikin gida, haɗe kuma da dakarun juyin juya hali mai kare gwamnatin ƙasar.

A zahiri ayyukan waɗannan biyu na kamanceceniya da juna. Alal misali rundunar juyin juya hali ta dage cewa ita ce da alhakin kwantar da tarzoma da kuma ci gaba da ƙarfafa rundunar sojin ƙasar, (na ƙasa da na sama da kuma na ruwa).

Cikin lokaci mai tsawo, rundunar juyin juya hali ta mayar da kanta rundunar soji mai ƙarfin gaske, da ke da tasiri a siyasa da tattalin arzikin Iran.

A halin yanzu shugaban rundunar ta IRGC, shi ne Manjo Janar Mohammad Pakpour, wanda jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei ya naɗa ranar 13 ga watan Yuni, bayan kisan Manjo Janar Hossein Salami, a wani hari da Isra'ila ta kai birnin Tehran.

An sake wa aikin rundunar fasali, bisa umarnin jagoran addinin ƙasar, ta yadda za ta fuskanci duk wata barazana ta cikin gida, tare da taimaka wa rundunar sojin ƙasar wajen magance barazana daga ƙetare.''

Hakan ya faru ne bayan haɗeWAR dakarun Basij (masu sa-kai) cikin rundunar ta IRGC.

An ƙiyasta cewa adadin dakarun juyin juya halin Iran ya kai 200,000, kodayake ana samun saɓanin alƙaluman daga mabambantan majiyoyi.

Rundunar na da dakarun sojin ƙasa baya da na ruwa da na sama, kuma ita ke kula da manyan makaman Iran.

Akwai wasu rundunoni da ke aiki da dakarun na IRGC da suka ƙara mata ƙarfi.

Dakarun Basij

Masu sa kai na rundunar Basij da ke aiki da rundunar ta IRGC ne ke tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati a ƙasar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masu sa kai na rundunar Basij da ke aiki da rundunar ta IRGC ne ke tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati a ƙasar

Babbar rundunar mai ƙarfi kamar yadda aka santa a ƙasar, rundunar Basij - mai aiki da dakarun juyin juya hali - na da yawan dakaru aƙalla 90,000 maza da mata

Rundunar na da ƙarfin da za ta iya tara ƴan sa kai aƙalla miliyan idan buƙata ta taso.

Ɗaya daga cikin manyan ayyukan rundunar Basij shi ne dakatar da tarzomar adawa da gwamnati a cikin ƙasar, kamar yadda ya faru a 2009 lokacin da tarzoma ta ɓarke bayan ayyana Mahmoud Ahmadinejad a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.

Magoya bayan ɗan takarar adawa, Mr Hossein Mousavi sun yi zargin rundunar da cuzguna wa masu zanga-zanga nuna damuwar bisa abin da suka bayyana da maguɗin zaɓe.

Haka kuma rundunar Basij ce ke da alhakin tabbatar da bin doka da oda a cikin ƙasar.

Dakarun Quds

Janar Qassem Soleimani ya jagoranci rundunar dakarun Quds, wani muhimmin sashe a rundunar IRGC kafin kashe shi a wani harin Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Janar Qassem Soleimani ya jagoranci rundunar dakarun Quds, wani muhimmin sashe a rundunar IRGC kafin kashe shi a wani harin Amurka

Dakarun Quds na ɗaya daga cikin sassan rundunonin IRGC, mai alhakin gudanar da wasu ayyukan rundunar a ƙasashen waje.

Rundunar Quds ce ke samar da makamai da bayar da horo ga ƙungiyoyin masu dauke da makamai da ke ƙawance da Iran, kamar Hezbollah a Lebanon, da ƙungiyoyin sa-kai a Iraƙi musamman bayan mamayar da Amurka ta yi wa Iraƙi a 2003.

Tsohon kwamandan rundunar Quds, Janar Qassem Soleimani, wanda jagoran addinin Iran Ayatolla Ali Khamenei ya taɓa yi wa laƙabi da ''rayayyen shahidi'' ya gina alaƙa mai ƙarfi tsakanin rundunar IRGC da ƙungiyoyi a ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya, irin su Yemen da Syria da Iraƙi da ma wasu.

Ya kasance ɗan Iran da ya fi fice da tasiri a waɗannan ƙasashe, kuma an riƙa ganin sa a lokuta da dama a fagen daga tare da mayaƙan Shi'a a Syria da Iraƙi a lokacin ƙoƙarin da suke na kafa Daular Musulunci.

Girman tasirin rundunar

Rundunar juyin juya hali na biyayya ga umarnin jagoran addinin Musulunci na Iran, wanda ke matsayin babban kwamandan rundunar sojin ƙasar.

Jagoran addinin ya yi amfani da ikonsa wajen faɗaɗa tasiri da ƙarfin rundunar ta hanyar naɗa jagororinta manyan muƙaman gwamnati a ƙasar.

An yi imanin cewa rundunar ce ke juya kusan kashi ɗaya bisa uku na tattalin arzikin ƙasar, baya ga riƙe ragamar manyan asusu da ƙungiyoyin agaji da wasu kamfanonin ƙasar.

Ita ce hukuma ta uku mafi arziki a ƙasar, baya ga hukumar kula da man fetur ta ƙasar da gidauniyar kula da wuraren ibada ta ''Imam Reza Endowment'', lamarin da ya bai wa rundunar IRGC damar ɗaukar matasa masu yawa aiki a ƙasar.

Ayyukan IRGC a ƙasashen waje

Duk da cewa dakarun IRGC ba su kai yawan na rundunar sojin ƙasar ba, ana yi mata kallon runduna mafi ƙarfi a Iran kuma ita ke jagorantar manyan ayyukan soji a ciki da wajen Iran.

Rundunar IRGC ta rasa wasu manyan jami'anta a lokacin yaƙin Syria, yayin da suke taimaka wa dakarun Bashar al-Assad da aka hambarar.

Haka kuma an yi imanin cewa rundunar IRGC na aiki a wasu ofisoshin jakadancin Iran a ƙasashen duniya, inda suke aikin tattara bayanan sirri, tare da samar da sansanonin horo, tare da bayar da tallafi ga ƙawayen Iran a ƙasashen waje.

Magoya bayan Hezbollah a Lebanon riƙe da hoton jagoran addinin Iran.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Magoya bayan Hezbollah a Lebanon riƙe da hoton jagoran addinin Iran.

Rundunar Quds ce tsagin IRGC da ya fi ƙaurin suna a ƙasashen waje.

Rundunar Quds ce ke samar da makamai da kuɗi da horo ga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a yankin Gabas ta Tsakiya.

"Dakarun Quds kan goyi bayan tsagin da ke samun goyon bayan Iran a wuraren da ake son sauyin gwmanatin da Iran ke goyon baya,'' a cewar Farfesa Alemzadeh.

Amurka na zargin dakarun Quds da ƙungiyoyin da take goyon baya da kashe ɗaruruwan sojin Amurka a Iraƙi da wasu wurare a yankin Gabas ta Tsakiya.

Majalisar Tarayyar Turai ta taɓa kaɗa ƙuri'ar amincewa da ayyana rundunar IRGC a matsayin ƙungiyar ta'addanci, to amma har yanzu ƙungiyar ta EU ba ta tabbatar da da matakin ba.

A shekarar 2019 ne Amurka ta ayyana rundunar IRGC a matsayin ƙungiyar ta'addanci, saboda jimawa da ta yi tana taimaka wa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai kamar Hezbollah.