Mene ne LRBM, mugun makamin da Iran ke yi wa Isra'ila ruwan wuta da shi?

a

Asalin hoton, EPA

Lokacin karatu: Minti 4

Bayan hare-haren da Isra'ilata ƙaddamar kan cibiyoyin nukiliyar Iran da kuma manyan sojojinta, Iran na mayar da martani ta hanyar harba manyan makamai masu linzami kan Isra'ila, inda wasu suka faɗa inda aka harba su.

Duk da cewa Isra'ila na cewa tana kakkaɓo da dama cikin makaman, wasu masu yawa sun samu tsallake tsaron sararin samaniyar ƙasar, inda suke faɗawa inda aka tura su, ciki har da Tel Aviv, babban birnin ƙasar, lamarin da ya haifar da gagarumar ɓarna da rasa rayuka.

Babu cikakkun bayanai game da girman makaman masu linzami da Iran ke amfani da su, to amma an yi imanin cewa makaman na ɗaya daga cikin manyan makamai masu haɗari da ake da su a yankin Gabas ta Tsakiya.

Waɗannan makaman sun bambanta dangane da tazarar da za su iya tafiya, akwai mai cin gajeren zango da ake yi wa laƙabi da SRBM.

Akwai kuma masu cin matsakaicin zango, da ake kira da MRBM/IRBM da kuma masu cin dogon zango, LRBM, waɗanda za su iya tafiyar dubban kilomita.

A wannan yaƙi da ke gudana tsakanin Iran da Isra'ila, ƙasar na amfani da waɗannan makamai, musamman mai cin dogon zangon, waɗanda suka zama mafiya muhimmanci ga ƙarfin Iran.

Yaya makamai masu linzami ke aiki?

Makamai masu linzami

Asalin hoton, European Photopress Agency

Iran ta riƙa ƙera mabambantan makamai masu linzami cikin fiye da shekara 30 da suka gabata, yayain da ƙasar ta zama ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya manyan makamai a yankin Gabas ta Tsakiya.

Makaman linzami masu cin dogon zango (LRBM), makamai ne da aka ƙera domin yin amfani da su da manufar samar da kawukan ko kuma linzami ga makaman nukiliya.

Ana harba irin waɗannan makamai ta hanyar amfani da waɗannan injunan makaman roka masu ƙarfin gaske, wanda shi ne yake harba su sama cikin gudu mai tsanani, su kuma yi tafiya mai nisa a sararin samaniya kafin daga bisani su dawo doron ƙasa.

Akan karkara harba su zuwa matakai daban-daban:

Mataki na farko akan tayar da injin domin ya ɗauki zafin da ake buƙata, daga nan sai a sanya rokokin a ciki a niƙa su domin rage musu nauyi, ta yadda za su ƙara gudu idan an harba.

Gudu, tazara da lokaci da makamin ke ɗauka

Makami mai linzami

Asalin hoton, Getty Images

  • Zangon makamin:

Makami mai linzami kan yi tafiyar tazara mai nisa, kama da kilomita 100 zuwa fiye da 10,000 tsakanin yankunan duniya.

Muhimmi daga cikinsu shi ne mai cin dogon zango LRBM, wanda ka iya tafiyar tazarar kilomita 3,500 zuwa 5,500, lamarin da ke haifar da barazana ga inda aka harba su.

  • Gudun makaman:

Waɗannan makamai kan yi gudun nan da Hausawa ke cewa na ''ƙifta wa da bismilla'', lamarin da ke ba su damar cimma dubban kilomitoci a cikin mintuna ƙalilan.

Akan auna gudunsu da wani ma'auni da ake kira ''Mach'', wanda ake kwatanta shi da gudun sauti (Mach ɗaya na gudu daidai yake da tafiyar kilomita 1,225), yayin da su kuma masu cin dogon zangon, LRBM kan yi gudun ''kifta wa da bismillah'', da ya zarta Mach biyar(tafiyar kilomita 6,125 cikin sa'a guda).

  • Lokacin da suke ɗauka suna tafiya:

Tazarar da ke tsakanin Iran da Isra'ila ta kai aƙalla kilomita 1,300 zuwa 1,500.

Makami mai linzami mai gudun Mach biyar daga Iran zai iya kaiwa Isra'ila cikin miti 12, kodayake haƙiƙanin lokacin ya danganta da irin makami da wurin da aka harba shi.

Me ya sa makamai masu linzami ke da wuyar kakkaɓowa?

s

Asalin hoton, Press Association

Bayanan hoto, Wani makami da bai kai mai linzami gudu ba

Abin da ya sa makamai masu linzami ke da hatsari shi ne kasancewarsu masu cin dogon zango, masu gudu da wahalar kakkaɓowa.

Gudun da suke yi idan an harba su ya sa na'urorin kakkaɓowa ba sa samun wadataccen lokacin kakkaɓo su, musamman idan suna faɗowa ƙasa idan suka iso wurin da aka aika su, suna faɗowa da sauri, lamarin da ya sa kakkaɓo su ke da matuƙar wahala.

Saɓanin sauran makamai da ake harbawa, da ke tafiya sannu-sannu, waɗanda ake kakkaɓowa cikin sauƙi, su makamai masu linzami kan yi gudu tare da jujjuyawa, lamarin da ke bai wa na'urorin kakkaɓowar wahala.

Yayin da wasu makaman kan ɗauki tazarar sa'a biyu daga Iran kafin su isa Isra'ila, su kuma jirage marasa matuƙa ke ɗaukar sa'a tara, su makamai masu linzami na da saurin gaske da hatsari saboda gudunsu da rashin iya kakkaɓo su cikin sauki.

Kuma makaman sun zama babban jigo a wannan yaƙin na Iran da Isra'ila.