Najeriya na da kashi 14 cikin 100 na mace-macen mata masu juna biyu a duniya — Minista

Mace mai juna biyu

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Ƙaramin ministan lafiya a Najeriya, ya bayyana cewa ƙasar na da kashi goma sha huɗu cikin ɗari na mace-macen mata masu juna biyu a duniya.

Dakta Iziaq Salako, ya bayyana haka ne a Abuja, yayin ƙaddamar da wani zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki game da inganta kiwon lafiya mai taken: "Dukkanmu mu haɗa hannu mu kyautata lafiyar al'ummar Najeriya."

Malam Salisu Yusuf, mamba ne a ƙungiyar da ke rajin inganta lafiyar mata masu juna biyu da ƙananan yara ta accountability mechanism for maternal and child health, ya shaida wa BBC cewa, bai kamata ace yanzu ana maganar waɗannan alkaluma ba, ya kamata ace an samu raguwa.

Ya ce,"kashi 14 cikin 100 na mace-macen mata juna biyu a Najeriya da minista ya faɗa gaskiya abu ne mai yawa kuma ya kamata a duba."

Malam Salisu ya ƙara da cewa bayanan ministan kamar akwai tufka da warwara domin wannan tsofafin alƙaluma ne, don a yanzu ana samun mata masu juna biyun da ke mutuwa fiye da yadda ministan ya faɗa.

Ya ce," A yanzu a cikin haihuwa dubu 100, ana samun mata 560 na mutuwa, haka a game da mutuwar kananan yara ma yanzu adadin da ministan ya faɗa ya fi haka."

"A don haka babban abin da ya kamata a yi shi ne yadda za a magance wannan matsala, na farko a samar da ingantattun asibitoci da kayan aiki da magunguna masu inganci da samar da ƙwararrun likitocin da ya kamata ace an samar domin shirin ko-ta-kwana."In ji shi.

Bayanai dai na cewa yawan mutuwar mata a yayin haihuwa a Najeriya ya yi tsanani kuma hakan na da nasaba da abubuwa da dama, kamar rashin tsarin kiwon lafiya mai ingancin, da ƙarancin magunguna, da tsadar aikin wanda ba kowa ne ke da ƙarfin biya ba, da yadda wasu ke saka al'adu da kuma rashin tsaro.

Matsalolin da suka shafi samun ciki ko haihuwa na ci gaba da kasancewa manyan kalubalen da bangaren lafiya a Najeriya ke fama da su, inda kasar ta ke da kashi tara cikin ɗari na mace-macen yara 'ƴan kasa da shekara biyar a duniya