Lafiya Zinariya: Abubuwan da ke janyo mace-macen mata masu juna biyu

Bayanan sauti
Lafiya Zinariya: Abubuwan da ke janyo mace-macen mata masu juna biyu

Dubun dubatan mata masu ciki ne ke rasa rayukansu a faɗin duniya, sakamakon wasu dalilai da suka shafi goyon ciki da kuma a yayin haihuwa.

Wasu matsaloli ne na kiwon lafiya, amma wasu dalilan, musamman ma a wasu kasashen nahiyar Afrika sun shafi al'adu da kuma talauci.

Wasu alƙaluman da hukumar lafiya ta duniya reshen Afrika ta fitar, sun nuna cewa, Najeriya ce ƙasa ta uku da aka fi samun mace-macen masu ciki a nahiyar. Inda mata 1047 suka mutu a cikin kowace haihuwa 100,000 da aka samu a ƙasar, a shekarar 2020.

Wasu bincike-binciken da aka gudanar a wata mujallar kiwon lafiya sun bayyana cewa jihar Katsina da ke arewa-maso-yammacin ƙasar, ta kasance a sahun gaba wajen mace-macen mata masu ciki.

Hukumar lafiya reshen Afrika ta ce a shekarar 2020 kaɗai an samu mutuwar mata masu ciki 531 a cikin kowace haihuwa 100,000 da akayi a nahiyar.

Lamarin da ke nuni da cewa nahiyar na kan gaba wajen matsalar mutuwar mata masu juna biyu a duniya.

Zuban jini matuƙa, cutar jijjiga, kamuwa da kwayoyin cuta, zubar da ciki na daga cikin abubuwan da ke ci gaba da janyo mutuwar mata masu juna biyu.