Shin duniya ta manta da Musulman Rohingya ne?

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yasmin ɗaya ce daga cikin dubban ƴan Rohingya da ba su samu ilimi ba

Cikin shekaru huɗu da ta yi a duniya, Yasmin ta kasance cikin rayuwa mara tabbas da rashin sanin makomarta. Ta kasa komawa ƙauyensu da ke Myanmar kasancewar an haife ta ne a sansanin ƴan gudun hijra a Bangladesh.

Zuwa yanzu, tana zaune ne a wani ɗaki mai duhu a Delhi, babban birnin India. Kamar dubban ƴan Rohingya - tsirarun ƙabilu a Myanmar - mahaifan Yasmin sun tsere daga ƙasar a 2017 domin kare kansu daga kisan kiyashin da sojoji ke yi. Mutane da dama sun tsere zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Bangladesh da India, inda suke zama a matsayin ƴan gudun hijra.

Shekara biyar bayan nan, Musulmin Rohingya - al'umma mafi yawa da ba ta da ƙasa, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya - na ci gaba da fuskantar wariya.

Mahaifin Yasmin, Rehman, ɗan kasuwa ne a Myanmar. Yayin da sojoji ke ƙaddamar da munanan hare-hare kan al'ymma, ya zama ɗaya daga cikin ƴan Rohingya 700,000 da suka tsere.

Bayan shafe kwanaki suna daɓa sayyada, Rehman da mai ɗakinsa Mahmuda sun isa sansanonin ƴan gudun hijrar da ke Cox Bazar, wani yanki a Kudu maso Gabashin Bangladesh da ke kusa da iyakarta da Myanmar. A nan, iyalin na zaune ne a cikin yanayi matsananci. Akwai matsalar ƙarancin abinci da kuma rashin tallafi.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rehman na fargabar lafiyar matarsa a don haka suka tsere zuwa Bangladesh

Shekara ɗaya bayan sun isa Bangladesh ne aka haifi Yasmin. Gwamnatin Bangladesh ta daɗe tana neman musulmin Rohingya su koma Myanmar. An sauya mazaunin dubban ƴan gudun hijra zuwa tsibirin Bhasan Char da ƴan gudun hijra suka bayyana a matsayin "tsibirin gidan gyaran hali".

Rahman na ganin ficewa daga zai taimaka wa ƴarsa samun makoma mai kyau. A 2020 kuma lokacin da Yasmin ta yi shekaru, iyayenta sun tsallaka zuwa India mai makwabtaka. An samu banbancin alƙaluma amma ƙungiyoyin ƴan gudun hijra na tunanin akwai ƴan gudun hijrar Rohingya tsakanin 10,000 da 40,000 a India.

Galibinsu sun kasance a ƙasar tun 2012. Tsawon shekaru dai ƴan Rohingya da ke nan na rayuwa cikin mutunci tattare da wata taƙaddama. Amma bayan da wani minista ya wallafa saƙon tuwita cikin wannan watan cewa za a samar wa da ƴan gudun hijrar gidaje da abubuwan more rauwa da kuma tsaro, sai kasancewarsu a Delhi ya ƙara janyo cece-kuce.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai ƴan gudun hijrar Rohingya tsakanin 10,000 da 40,000 a India
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sa'oi bayan nan kuma, gwamnatin India ƙarƙashin Jam'iyyar BJP mai mulki ta musanta yi wa musulmin Rohingya tayin kayayyakin ta kuma bayyana su a matsayin baƙi da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba waɗanda ya kamata a tusa ƙeyarsu ko kuma a tura su cibiyoyin tsare mutane."

Lamarin ya jefa iyalai irin na Rehman cikin damuwa. "babu tabbas a makomar ƴata, in ji shi yayin da zauna kan wani gadon katako mara katifa. "Gwamnatin India ma ba ta son mu...amma gwara su kashe mu a maimakon su mayar da mu Myanmar." "Babu ƙasar da ta shirya karɓar dubban ƴan Rohingya.

A makon da ya gabata ne Firaministan Bangladesh Sheikh Hasina ya fada wa hukumar kula da ƴan gudun hijra ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Michele Bachelet, cewa dole ne ƴan gudun hijrar da ke ƙasarta su koma Myanmar. Amma Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba za su iya komawa Myanmar ba saboda tashin hankalin da ake yi.

A Fabrairun 2021, sojoji da ake zargi da tafka laifuka kan al'ummar Rohingya sukja ƙwace iko da ƙasar a wani juyin mulki da suka yi. Ɗaruruwan yan Rohingya sun yi tafiya mai haɗari ta ruwa zuwa ƙasashe irinsu Malaysia da Philippines domin tserewa azabtarwar sojojin.

Adadin sansanonin ƴan gudun hijra a Bangladesh ya ƙaru zuwa kusan miliyan ɗaya. Rabin adadin yara ne. Kamar Rehman, ita ma Kotiza Begum ta tsare ne daga Mayanmar a Agustan 2017 - ya yi tafiyar kwana uku ba tare da cin abinci ba.

Ita da yaranta uku suna rayuwa ne a wani ɗaki da ke sansani a birnin Cox's Bazar. An rufe dakin da langa-langa da ke bai wa marasa galihu mafaka a lokutan ruwan sama.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kotiza da yaranta uku suna rayuwa ne a cikin sansanonin

Abubuwan tashin hankalin da ta baro a ƙauyensu ba su gushe daga zuciyarta ba. "Sojoji sun shiga gidanmu tare da azabtar da mu. Sai muka gudu bayan da suka buɗe wuta. An jefa yara cikin kogi. Suna kashe duk wanda ya biyo gabansu. Kamar wasu da suke sansanonin, Kotiza ta dogara ne kan tallafin abinci daga ƙungiyoyi masu zaman kansu da suke raba ganyen Lentil da shinkafa.

"Ba zan iya ciyar da su abincin da suke so ba, ba zan iya ba su kayan sawa masu kyau ba, ba zan iya kai su asibiti mai kyau ba," in ji ta. Kotiza ta ce wani lokacin tana sayar da abincin da ta samu domin sai wa yaranta biro da za su yi rubutu da shi.

A cewar wani nazari da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi a baya-bayan nan, rage tallafin da ƙasashen waje ke badawa ya ƙara dagula al'amura ga mutanen da suka dagora kacokan kan tallafin".

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ƴan gudun hijra na ci gaba da fuskantar ƙalubalen samun abinci mai gina jiki da wajen kwana da kuma tsafta da damarmakin aiki. Sannan ilimi - ɗaya daga cikin abubuwan da Kotiza ta fifita ga ƴaƴanta - na fuskantar gagarumar matsala.

"Yara na zuwa makaranta kullum amma babu wani ci gaba. Ina tunanin ba sa samun ilimi mai nagarta," in ji Kotiza. Ana koyawa yara da ke zaune a Cox's Bazar tsarin karatun ƙasarsu ta asali ba wai wanda ake koyarwa a makarantun Bangladesh ba.

Yayin da masu goyon bayan shirin suka ce zai taimakawa yaran wajen shiryawa komawarsu gida wata rana, wasu na fargabar hanya ce ta hana ƴan gudun hijrar Rohingya zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya da ƴan Bangladesh.

Idan suka samu ilimi, rayuwarsu za ta inganta. Za su yi aiki su kuma yi rayuwa mai cike da farin ciki," a cewar Kotiza.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubban ƴan gudun hijrar Rohingya, akasarinsu yara, suna zaune a sansanoni da ke Cox's Bazaar a Bangladesh

Wani tunani ne da Rehman ya yi a can Delhi yayin da yake riƙe da Yasmin mai shekara huɗu a hannunsa. "Na yi mafarkin na bata ilimi mai kyau da rayuwa mai inganci amma na gaza," yayin da ƴan Rohingya a duniya ke tunawa da kisan kiyashin da aka yi shekara biyar da suka gabata, har yanzu suna fatan za a yi musu adalci - ƙarar da aka shigar kan sojojin Myanmar na mala a Kotun duniya ta ICJ. Amma bayan wannan, suna da burin komawa gida.

Ƴan gudun hijra irinsu Rehman na roƙon ƙasashen duniya su kai musu ɗauki har zuwa lokacin da komai zai dai-daita su koma ƙasarsu. "Ban zo nan domin na yi sata ba, na zo ne domin kare rayuwata."