Musulman Rohingya sun maka Facebook a kotu suna neman diyyar $150bn kan kalaman kiyayya

Asalin hoton, Reuters
Gwamman 'yan Rohingya da ke gudun hijira a Birtaniya da Amurka sun gurfanar da kamfanin Facebook a gaban kuliya kan zargin iza wutar rikici a shafukan sada zumunta ta hanyar barin kalaman kiyayya a a kansu.
Sun bukaci Facebook ya biya su diyyar dala biliyan 150 kan ikirarin taka rawa wajen rura rikicin da ya kai aka kashe daruruwan Musulman Rohingya.
An yi kiyasin cewa an kashe Musulman Rohingya 10,000 lokacin da sojoji suka kaddamar da hare-hare a yankunan da mabiya addinin Buddha suka fi rinjaye a Myanmar a shekarar 2017.
Kawo yanzu kamfanin Facebook, wanda ya koma Meta, bai mayar da martani kan zarge-zargen ba.
Zargin ya biyo bayan wallafa kalaman kiyayya da batanci masu hadarin gaske da aka yi ta yadawa shekara da shekaru.
Kungiyar lauyoyi a Birtaniya da ke wakiltar 'yan gudun hijirar ta rubuta wasika ga Facebook, wadda BBC ta samu kan zarge-zargen da suka hada da:
- Facebook "ya yada kalaman kiyayya da aka yi ga kan 'yan Rohingya"
- Kamfanin "ya garara gudanar da bincike" kan masana siyasa da zamantakewa da halin da ake ciki a Myanmar
- Kamfanin ya gaza cire ko goge abubuwan da aka wallafa a shafin wadanda suka sake rura wutar rikicin da kara jefa Musulman Rohingya cikin hadari
- Ya gaza "daukar matakin da ya dace, a lokacin da ya kamata", duk da gargadin da kungiyoyin agaji da kafafen yada labarai suka yi kan halin da ake ciki a Myanmar
A Amurka lauyoyi sun shigar da korafi kan Facebook a San Francisco kan zargin "sanya rayuwar 'yan Rohingya cikin hadari, domin biyan bukatar kai, da samun kasuwa a 'yar karamar kasar da ke kudu maso yammacin Asiya.
Sun bayar da misali kan wani sako da aka wallafa a shafin Facebook da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa, ciki har da wanda aka yi a shekarar 2013 da ke cewa: "Mu yake su kamar yadda Hilter ya yaki Yahudawa."
Wani kuma na cewa: "Ku zuba musu fetur, ka na ku banka musu wuta, ta haka za su fi saurin isa ga Ubangiji."
Facebook yana da sama da mabiya miliyan 20 a Myanmar. Ga yawancinsu shafukan sada zumunta su ne kadai hanyar da za su yada labarai.
A shekarar 2018, Facebook ya amince cewa bai dauki matakan da suka kamata ba wajen kare kalaman kiyayya da tuzuri akan 'yan Rohingya.
Wannan ya biyo bayan wani rahoto da ba na gwamnati ba da Facebook ya gabatar da ke cewa shafin ya bayar da damar yin cin zarafin dan adam da iza wutar rikicin.

Sharhi - Daga Jamaes Clayton, wakilin BBC A Arewacin Amurka kan fasaha
Kura-kuran baya da Facebook ya yi na farautarsa
Abin da ya faru Myanmar shi ne abu na farko da ya fara shafawa Facebook kashin-kaji.
Shafin sada zumuntar yana da matukar farin jini a yankin - amma kamfanin bai fahimci ainihin abin da ke faruwa a shafin ba. Ba sa sake duba bayanan da aka wallafa da harshen mutanen Burma da Rakhine ke amfani da su.
Da sun bincika, da kuwa sun ga yadda ake ta wallafa kalaman kiyayya ga Musulmai, labaran karya da ake yadawa akan hare-haren da 'yan ta'addar Rohingya wai suka kai. Masu sukar lamiri sun ce wannan ya taimaka wajen iza wutar rikicin da ta kai ga mummunan tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar dubban rayuka.
Mark Zuckerberg da kan sa ya amince da cewa sun tafka kuskure, kan karuwar rikicin a Myammar.
Wannan ne ya sanya ainihin karar da aka maka facebook ta zama mai daukar hankali, kuma kamfanin bai musanta gazawarsa ba.
Ko ma yaya lamarin yake, a shari'ance sun taka rawa kan mummunan abin da ya faru da sanya rayuwar 'yan Rohingya cikin hadari. Abin tambayar shi ne ko tafiyar za ta yi nisa kan shari'ar? Watakila ta yi, watakila kuma ta bi shanun-sarki.
Sai dai Meta, na kokarin kawar da hankali daga Facebook saboda har yanzu kura-kuran da ya tafka a baya na ci gaba da farautarsa.

Ana kallon 'yan Rohingya, a matsayin 'yan gudun hijirar da suka je Myanmar ba bisa ka'ida ba, kuma cikin gwamman shekaru gwamnati da kanta ta nuna musu wariya.
A shekarar 2017, sojojin Myanmar suka kaddamar da hare-haren kakkabe 'yan Rohingya daga jihar Rakhine bayan wani mummunan hari da masu dauke da makan yankin sun kai w a 'yan sanda.
Dubbai ne suka mutu, yayin da wasu 700,000 suka tsere daga kasar zuwa makwabciyarta Bangladesh. Akwai kuma zarge-zargen da aka yi ta yadawa kan cin zarafin dan adam, ciki har da kisan gilla, da fyade da kona gidaje da gonaki da ake yi wa sojojin Myanmar.
Har wa yau, a shekarar 2018, Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Facebook da tafiyar hawainiya wajen daukar matakin gaggawa kan bayanan da ake yadawa a shafin.
Karkashin dokokin Amurka, Facebook na da babbar kariya kan daukar alhakin abin da masu amfani da shafin suka wallafa. Sai dai lauyoyin da suka shigar da sabon korafin sun ce babu wannan tanadin karkashin dokokin shari'a na Myanmar, don haka da su za a yi amfani wajen sauraren karar.
BBC ta tuntubi Meta kan ko mai zai ce game da hakan, amma bai ce uffan ba.












