Pakistan: Kisan dan Sri Lankan da ake zargi da batanci ga Annabi ya janyo zanga-zanga

Asalin hoton, EPA
Kisan gillar da aka yi wa wani dan kasar Sri Lanka da ake zargi da batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a Pakistan ya janyo zanga-zanga a kasashen biyu, inda shugaban Pakistan ya yi alla-wadai da tashin hankalin.
Priyantha Diyawadanage, mai shekara 48, manaja ne a wata ma'aikata da ke birnin Sialkot, an lakada masa duka har sai da ya mutu a ranar Juma'a sannan aka cinna wa gawarsa wuta.
Firaiministan Pakistan Imran Khan ya ce an kama sama da mutum 100 da ake zargi da hannu a aikata kisan.
Ya bayyana abin da ya faru a ranar da cewa "ranar abin kunya ce" a tarihin kasarsa.
Mai dakin mamacin, Nilushi Dissanayaka, ta yi kira ga gwamnatocin kasashen Pakistan da Sri Lanka su gudanar da cikakken bincike "a hukunta wadanda suka kashe min mijina uban 'ya'yana biyu".
"Na ga lokacin da ake caccakarsa a shafukan intanet... an wulakanta shi," in ji ta.

Kisan taron dangin da aka yi masa da aka yada a shafukan sada zumunta a karshen mako, da nuna yadda dandazon mutane suka kewaye wadanda suka yi ta jan Mista Diyawadanage a kasa tun daga ma'aikatar da yake aiki, tare da lakada masa duka har sai da ya mutu.
Daga nan kuma suka banka wa gawarsa wuta, yawancin wadanda suka yi dandazon sun yi ta daukar hoton dauki-da-kanka da gawar tana ci da wuta.
Me ya kai ga daukar mummunan matakin?
An faro tashin hankalin daga yada jita-jitar zargin wai Mista Diyawadanage ya yi batanci ga addinin Musulunci, inda ya cire takardun da aka manna a jikin bango, masu dauke da sunan Annabi Muhammad (SAW), kamar yadda wani jami'in 'yan sandan yankin ya bayyana.
Sai dai abokan aikinsa da suka garzaya inda lamarin ya faru domin ceto shi, sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP a Pakistan cewa Mista Diyawadanage ya cire takardun ne amma bai bai yaga su ba saboda ana shirin yin gyara a ginin.
Mai dakinsa ta musanta batun mijinta ya yi batanci ga addinin Musulunci.
"Ban amince da rahotannin da ke cewa mijina ya yaga takardun da aka lika a jikin ma'aikatarsu. Bai aikata abin da ake zarginshi da aikatawa ba," in ji ta a hira da BBC.
"Ya san ka'idoji da dokokin zama a Pakistan. Kasar musulunci ce. Ya san abin da ya kamta ya yi da wanda bai kamata ba, ya san yadda zai yi aikinsa, shekararsa 11 yana aiki a nan."
Yanayin kisan da aka yi a ranar Juma'a, da daruruwan mutane suka shiga ya girgiza kasar baki daya inda aka rika kiran a dauki mataki.
Firaiminista Imran Khan ya yi alla-wadai da abin da ya kira "hari irin na 'yan daba" tare da shan alwashin "hukunta duk wadanda aka samu da laifi kamar yadda doka ta tanada".
Ana daukar sabo a matsayin duk wani kalami da bai dace ba da za a yi wa addini ko ubangiji. A Pakistan, kuwa ana yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi batanci ga addinin musulunci.
Dokokin da kasar ke amfani da su, sun haramta batanci ga addinnin musulunci, da batanci ga fadar addini, da lalata wata alama da aka yi da ta shafi addini da gangan, da duk wani abu da ya shafi addinin musulunci.
Har wa yau, kalubalanta ko kalaman da ba su dace ba ga addini shi ma babban laifi ne, a shekarar 1982 ka ware wani sashe na musamman karkashin dokokin addini da suka halatta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga wanda ya wulakanta Al-Kur'ani.
A shekarar 1986, wani sashen a cikin dakar, ya bayyana hukuncin kisa ko daurin rai da rai, ga duk wadanda ya yi kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW)
A Pakistan zargin da ba shi da tushe bare makama, ka iya haddasa zanga-zanga, 'yan daba su samu damar daukar mummunan mataki ga wadanda aka zarga da aikata laifin.
An dade kungiyoyin kare hakkin dan adam na zargin an fi farwa mabiya addinai da ba su da rinjaye a cikin al'umma.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Mista Imran ya ce ya tattauna da takwaransa na Sri Lankan Shugaba Gotabaya Rajapaksa "domin nuna rashin jin dadi kan abin kunyar da ya faru ga mutanen Sri Lanka."
Hukumomin Sri Lankan, ba su ce uffan kan lamarin ba, watakil saboda gujewa karin tashin hankali da far wa musulmai a kasar.
An gaba ake sa ran kai gawar Mista Diyawadanage Sri Lanka, ana kuma sa ran yin wata zanga-zanga idan gawar ta isa babban birnin kasar Colombo.











