Hotunan wasu kayan Annabi Muhammad da ke gidan tarihin Turkiyya

Akwai wasu kayayyaki da Annabi Muhammadu SAW ya yi amfani da su a lokacin rayuwarsa da a yanzu haka suke wani gidan adana kayan a ƙasar Turkiyya.

Domin jin yadda waɗannan kayayyaki suke Turkiyya a yanzu maimakon birnin Madina na ƙsar Saudiyya inda Manzon Allah ya yi rayuwarsa, mun tuntuɓi Sheikh Ibrahim Daurawa, fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya kuma ƙwararre a fannin tarihi don jin yadda hakan ta kasance.

Malamin ya ce abubuwan da ake jinginawa Manzon Allah waɗanda aka same su a ƙasar Turkiyya sun samu ne a lokacin Sarki Abdulhamid II, a shekarar 1914.

Daular Usmaniyya ta kafu ne a shekara ta 1299, 27 ga watan Yuli, sannan ta ruguje a 29 ga watan Octoba shekara ta 1923, wato ta kwashe tsawon shekara 600 kenan tana gudana.

Wanda ya fara kafa ta kuwa shi ne Uthman na farko, wanda ake kiransa Attagul.

Wani sarki a lokacin yaƙin duniya ya so ya kai farmaki Madina domin ya yi ta'addanci, don haka wannan sarki ya sa aka tara sojoji masu yawa aka tura su domin su je su tsare Madina, su kuma kwaso duk wani abu da ke da alaƙa da Manzon Allah domin kada a maimaita ƙona alkyabbar Manzon Allah da Magul suka yi a Bagadaza.

Malamin ya ce shi yasa duk wani abu da ake jinginawa Manzon Allah sai aka kwashe su aka mayar da su Turkiyya domin samun kulawa ta musamman, d akuma kare su daga sharrin kafirai.

Sahun takun Annabi Muhammad kenan da aka nuna a wani gidan adana kayan tarihin musulmai dake birnin Santambul na Turkiyya a ranar 16 ga Nuwamban 2017. Gidan adana kayan tarihi na birnin Santambul dake unguwar Sultanahmet na ƙunshe da kayayyakin tarihi na Turkawa da na Musulunci. Sannan akwai tarin kayan kere-kere, na gilashi, da duwatsu da kayan kwalliya, da kayan karafa na yumɓu, da kuma manyan katifu na Turai, waɗanda kayan tarihi ne da ba safai ake samunsu daga bangarorin duniyar Musulunci ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sahun takun Annabi Muhammad kenan da aka nuna a wani gidan adana kayan tarihin musulmai dake birnin Santambul na Turkiyya a ranar 16 ga Nuwamban 2017. gidan dake unguwar Sultanahmet na ƙunshe da kayayyakin tarihi na Turkawa da na Musulunci. Sannan akwai tarin kayan ƙere-ƙere, na gilashi, da duwatsu da kayan kwalliya, da kayan ƙarafa na yumɓu, da kuma manyan katifu na Turai, waɗanda kayan tarihi ne da ba safai ake samunsu daga bangarorin duniyar Musulunci ba.
Takubban Annabi Muhammad da kuma gidajensu, da fitattun makera na zinare na Daular Usmaniyya suka yi wa wurin sanyawa, wannan hoton an dauke shi ne a ranar 3 ga watan Yulin 2018 a Turkiyya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Takubban Annabi Muhammad da kuma gidajensu, da fitattun makera na zinare na Daular Usmaniyya suka yi wa wurin sanyawa, wannan hoton an dauke shi ne a ranar 3 ga watan Yulin 2018 a Turkiyya
Wannan wata tasa ce, da aka yi imanin cewa Annabi Mohammed ya sha ruwa da ita, tana ɗaya daga cikin abubuwan da aka baje kolinsu a Fadar Topkapi da ke Santambul

Asalin hoton, Topkapi Palace Museum / TRTWorld

Bayanan hoto, Wannan wata tasa ce, da aka yi imanin cewa Annabi Mohammed ya sha ruwa da ita, tana ɗaya daga cikin abubuwan da aka baje kolinsu a Fadar Topkapi da ke Santambul
Hajrul Aswad, ko Baƙin Dutse da aka nuna a fadar Tokpati a ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 2018

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hajrul Aswad, ko Baƙin Dutse kenan, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga musulmin duniya, an nuna shi a fadar Tokpati a ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 2018
Mazubar ruwan Ka'aba kenan, wadda ita ma ka'aba kamar yadda aka sani ta na matukar muhimmanci ga al'ummar musulmin duniya, an nuna ta ne a fadar Topkapi Palace a ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 2018

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mazubar ruwan rufin Ka'aba kenan, wadda ita ma ka'aba kamar yadda aka sani tana da matuƙar muhimmanci ga al'ummar musulmin duniya, an nuna ta ne a fadar Topkapi a ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 2018

Gashin gemun Annabi Muhammad, da Hatiminsa da wasikunsa, da takubban Annabi Muhammad da gidajensu, na cikin wasu wuraren ajiya na musamman da maƙeran daular Usmaniyya suka samar, kuma ana nuna su ga dumin masoya Annabi Muhammad na duniya da mabiyansa, da kuma wasu sauran kayayyaki da ake alakantawa da sh

Silin gashin gemun Annabi Mohammed kenan, wanda ke da matuƙar tsarki ga al'ummar musulmi shima an nuna shi ne a Fadar Topkapi.

Asalin hoton, Topkapi Palace Museum / TRTWorld)

Bayanan hoto, Silin gashin gemun Annabi Mohammed kenan, wanda ke da matuƙar tsarki ga al'ummar musulmi shima an nuna shi ne a Fadar Topkapi.