Hotunan wasu kayan Annabi Muhammad da ke gidan tarihin Turkiyya

Akwai wasu kayayyaki da Annabi Muhammadu SAW ya yi amfani da su a lokacin rayuwarsa da a yanzu haka suke wani gidan adana kayan a ƙasar Turkiyya.

Domin jin yadda waɗannan kayayyaki suke Turkiyya a yanzu maimakon birnin Madina na ƙsar Saudiyya inda Manzon Allah ya yi rayuwarsa, mun tuntuɓi Sheikh Ibrahim Daurawa, fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya kuma ƙwararre a fannin tarihi don jin yadda hakan ta kasance.

Malamin ya ce abubuwan da ake jinginawa Manzon Allah waɗanda aka same su a ƙasar Turkiyya sun samu ne a lokacin Sarki Abdulhamid II, a shekarar 1914.

Daular Usmaniyya ta kafu ne a shekara ta 1299, 27 ga watan Yuli, sannan ta ruguje a 29 ga watan Octoba shekara ta 1923, wato ta kwashe tsawon shekara 600 kenan tana gudana.

Wanda ya fara kafa ta kuwa shi ne Uthman na farko, wanda ake kiransa Attagul.

Wani sarki a lokacin yaƙin duniya ya so ya kai farmaki Madina domin ya yi ta'addanci, don haka wannan sarki ya sa aka tara sojoji masu yawa aka tura su domin su je su tsare Madina, su kuma kwaso duk wani abu da ke da alaƙa da Manzon Allah domin kada a maimaita ƙona alkyabbar Manzon Allah da Magul suka yi a Bagadaza.

Malamin ya ce shi yasa duk wani abu da ake jinginawa Manzon Allah sai aka kwashe su aka mayar da su Turkiyya domin samun kulawa ta musamman, d akuma kare su daga sharrin kafirai.

Gashin gemun Annabi Muhammad, da Hatiminsa da wasikunsa, da takubban Annabi Muhammad da gidajensu, na cikin wasu wuraren ajiya na musamman da maƙeran daular Usmaniyya suka samar, kuma ana nuna su ga dumin masoya Annabi Muhammad na duniya da mabiyansa, da kuma wasu sauran kayayyaki da ake alakantawa da sh