Pakistan: Masu zanga-zangar ƙin jinin zanen ɓatancin Annabi Muhammad sun sake bazama tituna

Allo dauke da hoton jagoran kungiyar TLP, Khadim Hussain Rizvi, a ranar tunawa da mutuwarsa
Bayanan hoto, Allo dauke da hoton jagoran kungiyar TLP, Khadim Hussain Rizvi, a ranar tunawa da mutuwarsa
    • Marubuci, Daga Shumaila Jaffery
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Lahore

A watan jiya, Pakistan ta dage haramcin da aka kakaba wa jam'iyyar masu tsaurin Islama ta Tehreek-e-Labaik Pakistan (TLP a takaice), wadda ita ce ke jagorantar zanga-zangar kin jinin Faransa, kan sake yin zanen batanci ga Annabi Muhammad SAW. An sako shugaban TLP tare da magoya bayansa daga gidan kaso, sannan jam'iyyar na da 'yancin tsayawa takara a zabuka. Yawancin 'yan Pakistan dai na fargabar matakin ka iya shafar siyasar kasar da yankin ko ma duniya baki daya.

A ranar 31 ga watan Oktoba, an tura dan sanda Irfan Ahsan garin Wazirabad da ke yankin Punjab, domin tabbatar da tsaro a yankin da daruruwan 'ya'yan jam'iyyar suka yi zaman dirshan na mako guda da zanga-zanga da nufin isa fadar gwamanati da ke Islamabad, domin matsawa a kori jami'an diflomasiyyar kasar Faransa kan suke goyon bayan yada zanen batanci ga Annabi Muhammad SAW da wata mujallar kasar ta sake yi.

Masu zanga-zangar na kiran a saki jagoransu, Saad Rizvi, da ake tsare da shi karkashin dokokin yaki da ta'addanci.

'Yan jam'iyyar TLP sun sace Ahsan, lokacin da ya fita domin sayen magani a lokacin cin abincin rana, kamar yadda dan uwansa Usman Ahsan ya bayyana. Kwanki biyu da batan shi aka gano gawar shi da aka yi kaca-kaca da ita a wani asibiti da ke kusa da inda yake zama.

"Ranmu ya baci sosai, saboda wadanda suka kashe shin sun kira kansu musulmai, amma ba su amfani da koyarwar addinin musulunci ba, ban san wanne addinin musuluncin suke bi ba," in ji Mista Ahsan a hirarsa da BBC. "Sun lalata rayuwar iyalai da dama, sun mayar da 'yarsa marainiya, saboda kawai suna son a saki mutum daya."

Ba wannan ne karon farko da ake zargin jam'iyyar TLP da kisa irin haka ba. 'Yan sandan yankin sun ce a wannan shekarar kadai, magoya bayan TLP sun kashe 'yan sanda 10, da zabtarwa da ji wa mutum 1,300 mummunan rauni.

Su waye 'yan TLP?

Malamin nan mai tsattsauran ra'ayi Khadim Hussain Rizvi ne ya kafa kungiyar a shekarar 2015. Kungiyar addinin musulunci ce mai tsattsuran ra'ayi da kuma take goyon bayan dokar Pakistan mai cike da ce-ce-ku-ce ta hukuncin kisa ga wanda ya yi batanci ga Annabi Muhammad SAW.

A watan Nuwambar 2020 ne Khadim Hussain Rizvi ya mutu, bayan rashin lafiyar da ya fara lokacin da ya jagoranci zanga-zangar kin jinin Faransa a daidai lokacin da ake tsaka da annobar korona. Ya fusata kan kalaman Shugaba Emmanuel Macron na kare malamin makarantar nan da ya nunawa dalibai zanen batanci ga Annabi Muhammad SAW.

Dan Rizvi mai suna Saad Rizvi ne ya gaje shi, wanda ya ci gaba da nanata wa gwamnati bukatarsu da balle akala tsakanin Pakistan da Faransa. A zanga-zangar da suka gudanar a watan Afrilu sun rufe har da manyan hanyoyin da za su sada ka da birnin Islamabad. Gwamnati ta kama Rizvi, inda ta zarge shi da laifukan ta'addanci tare da daruruwan magoya bayansa.

'Yan uwan Irfan Ahsan rike da hotonsa, wanda aka tura tabbatar da tsaro a lokacin zanga-zangar da TLP suka yi
Bayanan hoto, 'Yan uwan Irfan Ahsan rike da hotonsa, wanda aka tura tabbatar da tsaro a lokacin zanga-zangar da TLP suka yi

Sauya salo

Sai dai watanni shida bayan nan, gwamnati ta sauya matsaya ta hanyar janye haramci ga jam'iyyar da sako daruruwan magoya bayanta ciki har da, Saad Rizvi. Gwamnatin ba ta yi bayanin dalilan da ya sa aka saki mutanen ba, sai dai kafafen yada labarai na bayar da rahoton ta yiwu babban janar din sojin kasar Qamar Javed Bajwa ya taka rawa wajen sakin mutanen.

Gwamnatin ta ce ta dauki matakin janyewa TLP takunkumi ne domin kaucewa tambayoyin da mutanen da ke ikirarin masoyan Annabi Muhammad SAW ne. Wasu masu sharhi na ganin cewa amfani da karfi da ya wuce kima kan kungiyar da ke ikirarin soyayya ga Annabi, wannan kuma ya karawa jam'iyyar su tagomashi.

Ministan yada labarai Fawad Chaudhr ya ce ci gaban da aka samu a baya-bayan nan ya nuna ba wai Indiya ce babbar barazanar ba, a'a 'yan ta'adda da ke kasar ne abin dubawa. "Yadda ta nuna goyon baya ga TLP, ya nuna masu tsaurin kishin islama ka iya dana tarko," in ji shi a lokacin da ya ke yi wa manema labarai bayani ga manema labarai a Islamabad.

Maimagana da yawun TLP Saddam Bukhari, ya yi ikirarin a lokacin da shugabanta Khadim Hussain Rizvi ya mutu a shekarar da ta gabata, magoya bayan shi daga sassa daban-daban ciki har da turai sun zo jana'izarsa.

Mai sharhi kan sha'anin tsaro Amir Rana, na cibiyar bincike da zaman lafiya ta Pakistan, ya ce yadda gwammnati ta tunkari TLP, bai dace da manufofin Pakistan na kasashen waje ba, sannan shigar TLP cikin jam'iyyun siyasa shi ba babbar matsala ce.

Babban taron magoya bayan TLP a Lahore, wadanda suka zo daga sassa daban-daban na duniya
Bayanan hoto, Babban taron magoya bayan TLP a Lahore, wadanda suka zo daga sassa daban-daban na duniya

TLP ta yi nasarar amfani da batun girmama Annabi Muhammad SAW wajen cimma muradunta, wanda daidai suke da na mabiya mazhabar Barelvi, wadda ta mamaye Pakistan. Amma za su kara amfani da wata damar wajen tabbatar da cewa sun zama a sawun gaba na jam'iyya mai krfin fada a ji a kasar.

Masu sharhi sun yi amanna cewa koyarwar da TLP ke dor mabiya na daga cikin abin da ke janyo mata farin jini tsakanin takwarorinsu, kuma hakan n kara ingiza kasar sake komawa turbar tsattsauran ra'ayin addinin musulunci.

Dr Hassan Askari Rizvi ya yi amanna siyasar Pakistan na tunkarar turbar da ta dace, duk da kara fadada ayyukan da TPL ke yi, kuma duk inda aka je aka dawo ba za ta yi nasarar samun karfin fada aji afannin siyasa ba.

Dole ne kungiyar ta shiga cikin kawancen wasu jam'iyyun, za mu jira mu ga matakin da za su dauka, da kuma inda suka nufa wajen sauya tsarin siyasar kasarm," in ji shi.

Wasu masu sharhi na ganin cewa, kungiyar TLP ka iya yin nasarar yin rinjaye, za ta iya samun isssun kuri'u ta fannin siyasa. Hakan kuma ba daddadan labari ne ka makomar siyasar Pakistan.