Sojojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 19 da aka sace a Abuja
An zaɓi sabon jagoran addinin Iran - Rahotonni
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza
Fafaroma Leo XIII ya buƙaci a tsagaita wuta a yaƙin Iran
Asalin hoton, Reuters
Jagoran ɗariar Katolika na duniya, Fafaroma Leo XIII ya ce ya yi matuƙar damuwa game da labaran da ke fitowa kan Iran da sauran ƙasashen Gabas ta Tsakiya.
Fafaroman ya yi kiran kawo ƙarshen yaƙin tare da komawa teburin sulhu.
Ba'amurken na farko da ya taɓa zama fafaroman, ya yi wannan kira ne a lokacin ibadar da ya jagoranta yau Lahadi a fadar Vatican.
Ya kuma gargain cewa yain zai iya bazuwa zuwa sauran asashen da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Mun kai hari sansanin jirage masu saukar ungulu a Kuwait - Iran
Asalin hoton, Reuters
Dakarun juyin juya halin Iran sun ce sun kai harin makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa kan sansanonin jirage masu saukar ungula na Al-Adiri da ke arewacin Kuwait.
Cikin wata sanarwa da dakarun suka fitar, sun ce sun lalata sansanin - wanda a nan ne ake shirya jirage masu saukar ungulu da gyara su da zuba musu da zuba wa manyan jirage mai.
Akwai dai sojojin Amurka da ke zama a sansanin, kamar yadda bayanai suka nuna.
Kawo yanzu Amurka da Kuwait ba su ce komai ba game da harin.
Amma ministan harkokin cikin gida na Kuwait ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta X News cewa an lalata jiragen yaƙi biyu a lokacin da suke aiki, kodayake bai bayar da cikakken bayani ba.
An kashe sojojin Isra'ila biyu a kudancin Lebanon
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Isra'ila, (IDF) ta ce an kashe dakarunta biyu a kudancin Lebanon.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Telegram, IDF ta bayyana sunan ɗaya daga cikin sojojin mai suna Maher Khatar, mai muƙamin babban saja, mai shekara 38.
IDF ta ce sojan, wanda ke aiki a sashen yaƙi na rundunar sojin ƙasar ya mutu ne yayin yaƙi a kudancin Lenbanon.
Sojojin na Isra'ila sun ce tuni aka sanar da iyalan ɗayan game da mutuwar tasa, amma dai har yanzu ba a kai ga wallafa bayanansa ba.
'An kai Isra'ilawa kusan 2,000 asibiti sakamakon hare-haren Iran'
Ma'aikatar lafiyar Isra'ila ta ce hare-haren Iran a ƙasar sun raunata mutum 1,929 tun bayan fara yaƙin a makon da ya gabata, inda aka kai su asibiti.
Daga cikin wannan adadi, har yanzu mutum 122 na kwance a asibiti, yayin da ta ce ''tara daga cikinsu na cikin mawuyacin hali''.
Sai dai ma'aikatar ta ce ba duka cikin adadi ba ne suka samu raunukan kai-tsaye sakamakon hare-haren makaman Iran masu linzami.
Ma'aikatar lafiyar ta ce a cikin kwana guda da ya wuce an yi wa mutum 157 magani a asibiti.
Rundunar sojin Isra'ila ta ci gaba da bayar da rahotonnin samun hare-haren makamai masu linzami daga Iran a shafinta na Telegram.
'Hare-haren Isra'ila sun kashe kusan mutum 400 a Lebanon'
Ma'aikatar lafiyar Lebanon ta ce adadin waɗanda suka mutu a ƙasar sakamakon hare-haren Isra'ila sun kai 394.
Yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai, ministan lafiyar ƙasar, Rakan Nassereddine ya ce cikin waɗanda suka mutu har da ƙananan yara 83 da mata 42 tun bayan da Lebanon ta shiga yaƙin da Amurka da ISra'ila ke yi da Iran.
Mista Nassereddine ya ƙara da cewa akwai ma'aikatan ceto tara cikin waɗanda suka mutun.
Labarai da dumi-dumi, An zaɓi sabon jagoran addinin Iran - Rahotonni
Ahmad Alamolhoda, mamba a majalisar magabatan Iran, ya ce majalisar ta zaɓi sabon jagoran addinin ƙasar.
Ya ce a yanzu ana jiran sakataren majalisar, Hosseini Bushehri, wanda ke da alhakin sanarwa duniya a hukumance ya sanar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Mehr na ƙasar ya ruwaito.
Iraniyawa sun yi maraba da ɗaukin da Amurka ta kai musu - Reza Pahlavi
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan gidan tsohon Shaa na Iran Reza Pahlavi ya ce Iraniyawa na matuƙar buƙatar abin da ya kira ɗaukin da Amurka da Isra'ila suka kai musu.
Cikin wata hira da kafar yaɗa labaran Fox News tsohon yariman ya nuna goyon bayansa kan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar a ƙasarsa.
''Miliyoyin Iraniyawa a ciki da wajen ƙasar sun ji daɗin wannan ɗauki da aka kai musu'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa hare-haren sun taimaka wa yanƙasar wajen ƙasa kusantar nasara da ƴanci fiye da baya.
Mai jagorantar hirar, Lara Trump, wadda suruka ce ga shugaban na Amurka, ta ce Shugaba Trump ya ce babban abin da ke gabansa shi ne Iran ta samu shugaba, ba batun dimokrɗiyya ba tukuna, inda ta tambayi yariman mulkin dimokraɗiyya yake so, ko akwai wani tsarin mulki da yake so wa ƙasar?
Sai ya ce dimokradiyya ce ta dace da Iran, ''saboda shi ne abin da miliyoyin Iraniyawa ke muradi''.
Ya ƙara da cewa ''babu wani tsarin mulki da zai dace da Iran fiye da dimokradiyya''.
''Hanyar da kawai al'ummar Iran ke so ita ce su riƙa zaɓar wa kansu makomar ƙasarsu da kansu'', in ji shi.
Sojojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 19 da aka sace a Abuja
Asalin hoton, Getty Images
Jami'an tsaron Najeriya sun ce sun kuɓutar da mutum 19 da aka yi garkuwa da su a Abuja, babban birnin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da sojojin ƙasar suka fitar ranar Asabar, sun ce sun kubutar da mutanen a lokacin wani samamen hadin gwiwar jami'an tsaron ƙasar a ƙauyen Gidan Dogo da ke yankin ƙaramar hukumar Bwari.
Sanarwar ta ce jami'an suin kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan maɓoyar ƴanbindigar da suka sace mutanen.
Sojojin sun ce an kashe mutum ɗaya cikin wadanda ake zargi da satar mutanen, yayin da sauran suka gudu, wasu da raunuka.
Satar mutanen domin neman kudin fansa na ci gaba da yawaita a ƴan shekarun nan a Najeriya, inda ƴanbindigar ke far wa garuruwa da tare kan manyan tituna domin satar mutane.
Duk da cewa a baya matsalar ta fi yawa yankin arewa maso yammcin ƙasar, a baya-bayan nan ta yi naso zuwa Abuja, babban birnin ƙasar.
'An kusa cimma matsaya kan magajin Ayatollah'
Asalin hoton, Telegram via Mehr News Agency
Wani bidiyo da kamfanin dillancin labari na Mehr mai alaƙa da ƙasar Iran ya wallafa, ya ambato wani babban malami na cewa majalisar magabatan Iran na dab da cimma matsaya kan wanda zai gaji tsohon jagoran addionin ƙasar, da aka kashe a makon da ya gabata.
Majalisar magabatan, ta ƙunshi manyan malamai 88 da aka zaɓa, domin su zaɓi sabon jagoran addinin ƙasar.
Kamfanin dillancin labaran na Mehr ya ambato Ayatollah Mohammad Mehdi Mirbagheri na cewa an kusa cimma matsayar, sai ƴan wasu abubuwa ƙalilan da suka rage.
Nan ba da jimawa ba ake sa ran majalisar ta za zauna, sai dai tuni sojojin Isra'ila suka yi gargaɗin farautar duka wanda ya zama magajin jagoran addinin.
'An fara samun tsaikon jigilar man fetur a Tehran'
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnan lardin Tehran na Iran ya ce an safa samun tsaikon jigilar man fetur a wasu sassan birnin sakamakon lalacewar hanyoyin jigilar.
Sai dai ya dage cewa an shawo kan matsalar.
A cikin daren da ya gabata ne KIsra'ila ta addamar da hare-haren makamai masu linzami kan rumbunan ajiyar man da kuma wasu yankunan birnin, yayain da mazauna birnin ke bayar da rahoton cewa gobara ta yaɗu zuwa gidaje da shaguna.
Sojojin Isra'ila sun ce tankokin man Iran na daga cikin cibiyoyin sojin ƙasar.
Yayin da aka lalata cibiyoyin soji da dama Iran, hare-haren Amurka da Isra'ila na ci gaba da faɗaɗa, inda firaministan Isra'ila ke cewa sun shirin ruguza gwamnatin Iran.
Isra'ila ta yi gargaɗi farautar wanda ya zama jagoran addinin Iran
Rundunar sojin Isra'ila ta yi gargaɗin ci gaba da farautar duk wanda ya gaji matsayin jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Cikin wani sako da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ''Mun samu bayanin cewa nan ba da jimawa ba majalisar manyan malaman Iran, wadda ta kwashe gomman shekaru ba ta yi zama ba, za ta yi taro a birnin Qom, don zaɓar sabon jagoran''.
"To muna son gaya musu cewa Isra'ila za ta ci gaba da farautar duk wanda ya gaji matsayin jagoran addinin ƙasar da kuma duk mutumin da ye nemi naɗa shi'', kamar yadda saƙon ya nuna.
"Don haka muna gargaɗin waɗanda ke shirin zuwa wanna taro cewa ba abin da zai hana mu kai musu hari. Wannan gargaɗi ne.'' a cewar sojojin na Isra'ila.
Trump ya ce ba ya neman taimakon Birtaniya a yaƙin Iran
Asalin hoton, EPA
A wani mataki na nuna fushinsa, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa ba ta buƙatar taimakon Birtaniya a yaƙin da take yi a Iran.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaba Trump ya ce Amurka ba ta buƙatar manyan jiragen dakon kaya na Birtaniya biyu a Gabas ta Tsakiya.
"Birtaniya, ɗaya daga cikin manyan ƙawayenmu, watakila ma babba cikin ƙawayen namu, a yanzu na nuna shakku kan tura manyan jiragensu biyu zuwa Gabas ta Tsakiya. Amma ba komai'', kamar yadda ya wallafa.
''Amma firministan Birtnaiya ka sanin mu yanzu ma ba ma buƙatarsu - Amma za mu riƙa tuna wannan. Mu ba ma son ma mutane su shigar mana yaƙi bayan mun riga mnun yi nasara''.
Wanna na zuwa ne bayan Staemer ya ƙi amincewa Amurka ta yi amfani da sansanonin sojin Birtaniya a yankin Gabas ta Tsakiya don kai wa Iran hare-hae.
Daga baya Trump ya ce ''Ba ya son taimaka mana''.
“Ban taɓa tsammanin haka ba, ban taɓa tsammanin Birtaniya za ta yi mana haka ba,'' kamar yadda ya shaida wa Jaridar The Sun.
Gwamnatin Birtaniya dai ba ta shiga yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran ba, sannan ba ta yi alƙawarin shiga ba.
An samun ƙarin manyan fashe-fashe cikin dare a Iran
Asalin hoton, Reuters
Karin fashe-fashe cikin dare sun girgiza biranen Iran a wasu ƙarin jerin hare-hare da Amurka da Isra'ila ke kai wa ta sama.
An ga ɗimbin hayaƙi ya turnuƙe sama cikin dare, bayan da aka kai hari kan wasu wuraren adana mai a ciki da kewayen Tehran, babban birnin ƙasar.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai abin da ta kira hare-hare da dama, kan rumbunan mai, da ta ce sojin Iran na amfani da su.
An kai wasu hare-haren ma kan cibiyoyin mai a lardin Alborz.
Yadda hare-haren suka lalata wuraren da aka hara da dama, akwai alamun faɗaɗa yaƙin na Amurka da Israila, inda Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya ce, akwai tsarin da suke bi daki-daki na durƙusar da gwamnatin ta Iran
Iran ta ci gaba da kai wa makwabtanta hare-hare
Asalin hoton, ...
Makwabtan Iran sun ci gaba da fuskantar hare-haren makamai masu linzami da na jiragen sama marasa matuƙa, duk da sanarwar da shugaban Iran ya yi kan alkawarin cewa, za a kai musu hari ne kawai idan su suka fara kai wa Iran ɗin.
An kai hari kan wani rumbun ajiyar mai a babban filin jirgin sama na Kuwait, amma hukumomi sun ce, an yi nasarar kashe wutar da ta tashi.
Haka ita ma Bahrain, wuta ta tashi a tashar jirgin ruwanta ta Salman.
A ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa, an samu rahoton mutuwar mutum ɗaya, yayin da su ma ƙasashen Saudiyya da Qatar suka fuskanci hare-haren.
An samu sanarwa daga shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda a karon farko ya yi magana a fili -inda ya ce Ƙasar na cikin yaƙi.
An harba makaman roka kan ofishin jakadancin Amurka, da ke babban birnin Iraqi, Baghdad, kamar yadda shi ma wani ginin Majalisar Dinkin Duniya a yankin Kurdistan na Iraqin aka kai masa harin.
Assalamu alaikum
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.