Gwajin cutar HIV da juna biyu a kan masu neman aikin haraji a Kenya ya janyo ce-ce-ku-ce

‘Yan majalisar dokokin Kenya suna gudanar da bincike a kan daukar ma’aikatan haraji, bayan da ta bayyana cewa an ki daukar wasu bayan da aka yi musu gwajin cuta mai karya garkuwar jiki da kuma gwajin juna biyu.

Hukumar haraji ta kasar ta ce, ta ki amincewa da sama da mutum 130 da suka nemi aikin na tattara haraji, bayan da aka yi musu gwajin a shekarar da ta wuce.

Daukar aikin na daga yunkurin gwamnatin kasar na kara samun kudade, da kuma maganin masu kin biyan haraji.

Hukumomin kasar ta Kenya sun ce aikin na daukar masu karbar haraji, aiki ne da yake bukatar mutane masu karfi da azama da kuma cikakkiyar lafiya, saboda haka duk wanda aka dauka sai an ba shi horoi na soja, saboda kalubalen da ke tattare da aikin.

Hukumomin suka ce gwajin cuta mai karya garkuwar jiki da kuma na juna biyu, abu ne da daman a ka’ida ake yi wa duk wanda zai yi aikin soja, kuma aikin na karbar haraji aiki ne da yake tamkar na soja.

To sai dai a karkasjhin dokokin kasar ta Kenya ba daidai ba ne a nuna wa mutum wariya ko bambanci a kan yanayi ko matsayin lafiyarsa, idan za a dauke shi aiki.

Jin labarin cewa an rika yi wa wadanda za a dauka aiki gwajin lafiya, ya bata ran wasu ‘yan majalisar dokokin kasar ta gabashin Afirka, a lokacin zamanta.

Wata kungiyar kare hakki ta kasar ta ce wannan ka-ce-na-ce, ya nuna a fili cewa ‘yan Kenya ba masu ci gaba ba ne kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar yake.

Kwamishinar hukumar tattara harajin cikin gida ta kasar, Rispah Simiyu, ta kare matakin yin gwajin.

Ta ce, gwajin wanda rundunar sojin kasar ta gudanar a kan masu neman aikin karbar harajin, 1,406 abu ne da aka saba saboda ma'aikatanta kusan irin kalubalen da ke gabansu kamar na masu kayan sarki ne.

Wato aiki ne da ke bukatar cikakkiyar lafiya da kuma kare lafiyar mutum a lokacin horon don gudun samun matsala.

Babban shugaban hukumar harajin kasar, Humphrey Wattanga ya gaya wa ‘yan majalisar cewa mutum sama da 133 din da aka ki dauka saboda gwajin, ba wai an nuna musu wariya ba ne saboda halin da aka same su, kuma ya ce sakamakon nasu abu ne na sirri.

Amma duk da haka ‘yan majalisar dokokin sun bukaci sanin dalilin da ya sa aka ki su, saboda yadda dokar kasar ta haramta nuna bambanci wajen daukar aiki saboda matsayin lafiyar mutum.

A watan nan ne wata kotu a kasar ta Kenya ta soke daukar aikin masu karbar haraji sama da dubu daya, saboda a cewarta wadanda aka dauka ‘yan kabilun shugaban kasar ne da kuma mataimakinsa.