Kenya ta zabtare yawan jami'an tsaron tsohon shugaban ƙasar

Kenya ta rage yawan jami’an tsaro da ke bai wa tsohon shugaban ƙasar Uhuru Kenyatta kariya, a daidai lokacin da dangantaka ke ƙara tsami tsakaninsa da wanda ya gaje shi bisa kiraye-kirayen a yi bincike kan batun biyan haraji na iyalan Kenyatta mai ɗimbin arziki.

Shugaban ‘yan sandan ƙasar ya faɗa wa manema labarai cewa an yi sauye-sauyen ne bisa ka’idojin ‘yan sanda kan tsaron shugaban da ya yi ritaya.

"Yana da isasshen tsaro, duk abin da aka yi, an yi shi ne da manufa mai kyau,’’ in ji Japheth Koome, Sifeton ‘yan sandan ƙasar a wata tattaunawa a ranar Juma’a.

Jaridar Daily Nation ta ruwaito cewa an rage yawan jami’an tsaron mista Kenyatta guda 96 wanda ya kunshi kwararrun jami’ai zuwa 25 yayin da na mai ɗakinsa kuma zuwa guda biyar.

An kuma rage jami’an tsaron tsoffin ministoci masu faɗa a ji lokacin mulkin Kenyatta.

Ƙawayen Shugaba Ruto na ta kiraye-kirayen gudanar da bincike kan harajin da aka yafe da iyalan Kenyatta suka ci gajiya lokacin mulkinsa.

A makon nan ne shugaba Ruto ya zargi waɗanda suka ki biyan haraji da tallafa wa zanga-zangar ‘yan adawa a baya-bayan nan.