Jihohin Najeriya da 'yan ƙwadago suka shiga yajin aiki

Takardun naira

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Duk da cewa jihohi da dama sun amince da N70,000 ko fiye a matsayin mafi ƙarancin albashi, da yawansu ba su fara biya ba kwatakwata, ko kuma wani ɓangare suka fara biya
Lokacin karatu: Minti 3

Ƙungiyoyin ƙwadago a wasu jihohin Najeriya sun tsunduma yajin aiki saboda rashin fara biyan naira 70,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi da gwamnonin jihohin suka yi.

Matakin ƙungiyoyin biyayya ce ga wa'adin da gamayyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa wato Nigeria Labour Congress (NLC) ta saka na ranar 1 ga watan Disamba ga jihohi kusan 14 da ba su fara biyan sabon albashin ba ga ma’aikatansu.

A ranar 29 ga watan Yulin 2024 ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya tabbatar da sabon albashin bayan ya saka hannu kan dokar da aka yi wa kwaskwarima tare da alƙawarin za a dinga sake duba ta duk bayan shekara uku.

Rahotonni sun ce biyar daga cikin jihohin da ba su fara biyan albashin ba ne suka shiga yajin aikin, waɗanda suka haɗa da Kaduna, da Nasarawa, da Zamfara, da Ebonyi, da kuma birnin tarayya Abuja.

Sai kuma tara daga cikinsu da suka ce ba za su shiga ba saboda suna tattaunawa da gwamnatocin jihohin nasu.

Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa yajin aikin ya fara tasiri, inda ya tilasta wa wasu jihohin fara neman ‘yan kwadagon domin tattaunawa da su kan fara biya nan ba da jimawa ba.

Jihohin da ba su fara biya ba

Duk da cewa jihohi da dama sun bayyana amincewa da N70,000 ko fiye, da yawansu ba su fara biya ba kwatakwata, ko kuma wani ɓangare suka fara biya na matakin albashin.

Tun a watan Oktoba gwamnatin Katsina ta ce ta amince da biyan sabon albashin, amma sai a ranar Asabar Gwamna Dikko Radda ya sanar cewa sai a watan Disamba za a fara biya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Haka ma gwmanatin jihar Nasarawa, wadda ta ce za ta fara biyan N70,500 nan gaba. A jihar Ondo kuwa, sai a watan Nuwamba ne NLC ta ce za a fara biyan ma'aikatan bayan amincewa da N73,000 tun a watan Oktoba.

Ƙungiyar ƙwadago reshen jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta fara biyan albashin amma ba bisa yarjejeniyar da suka amince ba.

"Mun yi yarjejeniya cewa za a bai wa mai matakin albashi na ɗaya N72,000, mai mataki na biyu za a ba shi N73,000 har zuwa ƙarshen tsanin aikin gwamnati, amma sai gwamnati ta yi abin babu tsari," in ji Kwamred Ayuba Suleiman, shugaban NLC a Kaduna.

"Sun fara biya amma ba a kan yadda muka yi yarjejeniya ba. Ka san aikin gwamnati mataki-mataki ne, kuma a nan ne aka samu matsala," a cewarsa.

Sai dai gwamnatin jihar ta ce tangarɗar na'ura ce ta haifar da matsalar, kamar yadda Shugaban Ma'aikatan jihar Kaduna Sani Liman Kila ya shaida wa BBC.

Bayanai na nuna cewa jihohin da ko dai ba su fara biyan albashin ba kwatakwata ko kuma ba su biya duka ba sun ƙunshi: Abia, Akwa Ibom, Ebonyi, Ekiti, Imo, Nasarawa, Kaduna, Katsina, Oyo, Cross River, Sokoto, Yobe, Zamfara, Enugu, sai kuma birnin tarayya Abuja.