West Ham ta tuntubi Manchester United kan batun Jesse Lingard

Jesse Lingard

Asalin hoton, Getty Images

West Ham United ta tuntubi Manchester United, don jin halin da Jesse Lingard ke ciki, wanda kwantiraginsa zai kare a Old Trafford a makon gobe.

Koci, David Moyes na son daukar dan kwallon tawagar Ingila, mai shekara 29 wanda ya taka rawar gani a wasannin aro da ya yi wa West Ham a bara.

Tun daga lokacin sau biyu Moyes ya yi kokarin mallakar dan kwallon, amma United ba ta sallama ba.

Lingard ya sanar cewar an yaudare shi kan halin da aka nuna masa a wata 12, ya kuma yanke shawarar barin United, duk da daukar sabon koci, Erik ten Hag.

Kungiyoyi da dama a Premier League da wasu daga wajen Ingila sun yi ta zawarcin dan kwallon a kaka biyun da ta wuce.

United ta hana Lingard barin kungiyar, wanda Ole Gunnar Solskjaer ya yi ta rarrashi, shi kansa Ten Hag ya ce zai duba batun Lingard yadda zai biya masa bukatunsa.

Wasa biyu kacal Lingard ya buga a Premier League a bara, ya kuma yi fushi da Ralf Rangnick bai saka shi a karawar da United ta doke Brentford 3-0 ba a Old Trafford.

Dan kwallon ya so buga fafatawar, domin ta zama ta ban kwana da magoya bayan Manchester United.

Lingard bai buga wasa hudun karshe da aka karkare kakar Premier League ta bana ba.