Karim Benzema: Dan wasan Real Madrid ya tsawaita kwangilarsa

Asalin hoton, Getty Images
Kyaftin din Real Madrid ya tsawaita yarjejeniyarsa domin ci gaba da kasancewa da kungiyar ta Bernabeu har zuwa shekara ta 2023.
Hakan shi zai sa dan kwallon ya kasance a Real na tsawon shekaru 14.
Benzema, mai shekaru 33, ya je Real Madrid ne a shekara ta 2009 inda ya zura kwallo 281 kawo yanzu.
Dan wasan na Faransa shi ne na biyar a cikin jerin masu yawan zura kwallo a Real.
Sabunta kwangilar ta yi daidai ta matakin da golan Belgium, Thibaut Courtois wanda ya tsawaita kwangilar har zuwa shekarar 2026.







