Emerson Palmieri: Mai tsaron bayan Chelsea ya je aro Lyon zuwa karshen kakar bana

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron baya a Chelsea, Emerson Palmieri ya je buga gasar Ligue 1 ta Faransa da zai yi wa Lyon wasannin aro zuwa karshen kakar bana.
Mai shekara 27, wanda ya lashe Euro 2020 a tawagar Italiya a bana, ya koma taka leda a Chelsea daga Roma a Janairun 2018.
Ya buga wa kungiyar ta Stamford Bridge wasa 71, ya kuma bayar da gudunmuwa da Chelsea ta ci Champions League da Europa League da kuma Super Cup.
Lyon tana mataki na 17 a kasan teburin gasar Faransa, bayan samun maki daya tal a fafatawa biyu a kakar bana.







