Gwarzon dan kwallon Turai: Jorginho da Kante da De Bruyne

Chelsea's Jorginho and N'Golo Kante and Manchester City's Kevin de Bruyne

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kevin de Bruyne da Jorginho da kuma N'Golo Kante sun buga wasan karshe a Champions League a bara

'Yan wasan Chelsea, Jorginho da N'Golo Kante da Kevin de Bruyne na Manchester City, sune ke takarar kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Turai na bana.

An kuma fitar da kocin Chelsea ta mata Emma Hayes da tsohon kocin Barcelona ta mata, Luis Cortes da na tawagar mata ta Sweden, Peter Gerhardsson a matakin masu takarar kocin mata da ke kan gaba. .

A bangaren maza kuwa an bayyana mai horar da Manchester City, Pep Guardiola da na Chelsea, Thomas Tuchel da na tawagar Italiya Roberto Mancini a matakin masu takarar mai horarwa da yafi fice.

Matan 'yan wasa da ke takarar gwarzuwar 'yan kwallon kafa ta Turai ta bana sun kunshi 'yan Barcelona uku da suka lashe Champions League, Jenni Hermoso da Lieke Martens da kuma Alexia Putellas.

Wannan shine karon farko tun bayan shekara 11 da aka samu masu takarar gwarzon dan kwallon kafa na Turai uku masu buga wasa daga tsakiya.

Jorginho da kuma Kante sun lashe Champions League tare da koci Tuchel a Chelsea, bayan da suka doke De Bruyne da Guardiola mai horar da Manchester City a wasan karshe.

Jorginho ya kuma lashe gasar cin kofin nahiyar Turai wato Euro 2020 a tawagar Italiya tare da koci Mancini.

Dan kwallon Bayern Munich, Robert Lewandowski shine ya lashe kyautar bara.

Mai horar da kungiyar Chelsea ta mata, Hayes ta ja ragamar Chelsea karo hudu cikin kaka tara da ta yi zuwa Champions League har da kai wa wasan karshe a kakar da ta wuce.

Za a sanar da wadanda suka zama zakaru a lokacin da za a yi bikin raba jadawalin gasar Zakarun Turai a Instanbul ranar Alhamis 26 ga watan Agusta.