Ko Rohr zai gayyaci Ahmed Musa zuwa Super Eagles?

Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images

Kocin tawagar kwallon kafa ta Najeriya, Gernot Rohr ya ce Kyaftin Ahmed Musa zai samu wata kungiyar da zai koma buga tamaula nan gaba.

Sai dai kocin bai ce komai ba kan batun ko zai bai wa dan kwallon goron gayyata a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da Najeriya za ta yi nan gaba.

Mai shekara 28 bai da kungiyar da yake da yarjejeniya da ita, tun bayan da ya bar Al Nassr ta Saudi Arabia cikin watan Oktoba.

An dade ana ta rade radin cewar tsohon dan wasan Leicester City zai koma taka leda a kasar Ingila.

Likitoci sun amince da koshin lafiyar dan wasan a West Bromwich Albion wadda ta janye daga shirin kulla gajeriyar yarjejeniyar, saboda baya kan ganiya.

Rohr bai ce ko zai gayyaci Musa cikin 'yan wasan da za su buga wa Najeriya karawar neman shiga gasar kofin nahiyar Afirka da za ta yi da Benin da kuma Lesotho ba.

Cikin watan Nuwamba, Musa wanda bai da kungiya a lokacin yana cikin 'yan kwallon Super Eagles da suka kara da Saliyo gida da waje, lamarin da ya sha suka daga 'yan jarida.

Musa tsohon dan kwallon Kano Pillars, shi ne kyaftin din Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Afirka da kasar ta yi ta uku a Masar a 2018.