Karanta tarihin karawar Super Eagles da Chipolopolo?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Abdulwasiu Hassan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
A yau ne tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eaglesta doke takwararta ta Zambiya, wato, Chipolopolo da 1-0, lamarin da ya sa Najeriya ta samu shiga gasar cin kofin duniya da za a buga a Rasha a shekarar 2018..
Najeriya ta samu zuwa Rasha ne bayan ta samu shiga gasar a shekarar 1994 da 1998 da 2002 da 2010 da kuma 2014.
Ita kuwa Zambiya ba ta taba shiga gasar, kuma a ta kasa raya fatanta na zuwa gasar a karon farko bayan ta sha kaye a hannun Najeriya.
Sai dai kuma tarihin fafatawan da kungiyoyin suka yi ya kafin wasan da suka yi yau, ya nuna cewar Najeriya ta fi Zambiya yin nasara.
Najeriya ta doke Zambiya sau shida ( a ranar 11 ga watan Nuwambar 1973 da 12 ga watan Maris 1990 da 10 ga Afrilun 1994 da 13 ga watan Janairun 2001 da 25 ga watan Janairun 2010 da 15 ga waatan Nuwambar 2011 da kuma 9 ga watan Oktoban 2016).

Asalin hoton, Getty Images
Ita kuma zambiya ta doke Najeriya sau biyar ( a ranar 28 ga watan Oktoban 1973 da 28 ga watan Yulin 1981 da 13 ga watan Maris 1982 da 18 ga watan Augustan 1985 da kuma 15 ga watan Disamban 1997).
Kasashen kuma sun yi canjaras a wasanni biyar ( a ranar 10 ga watan Maris na 1978 da 10 ga watan Agustan 1985 da 17 ga watan Disamban 1997 da 24 ga watan Maris 2001 da kuma 25 ga watan Janairun 2013).
Bayan sun kece reni, Najeriya ta kara wa zambiya tazara a adadin nasarar da ta yi kanta.
Yanzu sau bakwai kenan Najeriya tana samun galaba akan Zambiya fagen tamola.












