Premier League: Kyaftin din Villa Jack Grealish ya amsa laifin tuƙin ganganci

Asalin hoton, PA Media
Wata kotu da ke zamanta a Birmingham ta kama dan wasan Ingila kuma kyaftin din Aston Villa da laifin tuƙin ganganci.
Grealish mai shekaru 25 ya amsa laifin tuƙin gangancin har sau biyu a cikin wannan shekara.
Laifin na farko da aka tuhume shi da shi ya faru ne a ranar 29 ga watan Maris, a lokacin kullen Korona.
To sai dai bayan tukin na farko da har ya janyo haɗari, kotun ta kama Grealish da irinsa a ranar 18 ga watan Oktoba, wanda shi kuma ya faru a kusa da filin atisayen ƙungiyarsa wato Aston Villa.
Duk da ɗan wasan bai bayyana a zaman da kotun ta yi ba, Jack Grealish ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su ta hannun lauyansa.
Bugu da kari, kotun ta kama shi da laifin ƙin ankarar da hukumomi game da haɗarin da tuƙin gangancin ya haddasa.

Asalin hoton, PA Media
A yanzu kotun ta saka ranar 15 ga watan Disamba don yanke hukunci, kuma tuni lauyansa ya sanar da kotun cewa Jack Grealish ba zai samu halartar zaman ba.
Akwai yiyuwar kyaftin din na Aston Villa zai fuskanci dakatarwa daga tuƙa mota.











