'Yan kallo za su fara shiga filin wasa a Ingila

Watanni takwas kenan rabon da yan kallo su shiga kallon wasanni a Ingila, a lokacin da annobar Korona ta yi kamari a Burtaniya.
Bayanan hoto, Wata takwas kenan rabon da 'yan kallo su shiga kallon wasanni a Ingila saboda bazuwar annobar Korona

Za a bai wa 'yan kallo akalla 4,000 damar shiga filaye don kallon wasa a wuraren da annobar Korona ba ta yi muni ba a Ingila.

Da ma a na cikin dokar kulle ta mako hudu a duk fadin Ingila, wadda za ta kare a ranar 2 ga watan Disamba.

Ana sa ran Firanminista Boris Johnson zai sanar da damar shiga filin wasa ga 'yan kallon a hukumance a yau Litinin.

Sai dai duk da damar da gwamnatin ta bayar, za a jira sakamakon kuri'ar da 'yan majalisa za su jefa kan batun kafin mako ya kare.

Haka ma za a bar 'yan kallo 2,000 shiga kallon wasa a wuraren da annobar Korona ta yi ƙamari sosai, yayin da wasu wuraren za su hakura sai yadda hali ya yi.

Wannan mataki na daga cikin sauye-sauyen da ake hasashen za a yi a sabuwar dokar kullen Korona da gwamnati za ta sanar.

Wata takwas kenan rabon da 'yan kallo su shiga kallon wasanni a Ingila sakamakon ƙamarin da annobar Korona ta yi a Burtaniya.