Barcelona: Dan wasan baya Gerard Pique zai yi jinyar wata uku zuwa biyar

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Pique ya fita daga wasan bayan dawowa hutun rabin lokaci a fusace

Dan wasan bayan Barcelona Gerad Pique zai yi jinyar wata uku zuwa biyar sakamakon raunin da ya ji a gwiwarsa.

Pique mai shekara 33, ya samu raunin ne a gwiwar kafarsa ta dama yayin wasan Barcelona da Atletico Madrid a ranar Asabar.

Kazalika, Barcelona za ta ci gaba da wasa ba tare da ɗan wasan bayanta ba Sergi Roberto har nan da tsawon wata biyu, shi ma saboda ciwon da ya ji a cinyarsa.

Rashin nasarar da Barcelona ta yi a wannan mako, shi ne na uku da ta yi cikin wasa takwas na La Liga da ta buga, kuma a yanzu tana matsayi na 10 a jerin jadawalin gasar.

Kungiyar dai na fuskantar koma-baya tun farkon fara wannan kakar wasan, inda wasu da dama ke alaƙanta hakan da rikicin Lionel Messi da mahukuntan ƙungiyar.

Wannan rikici ne ya yi sanadiyyar ficewar shugaban ƙungiyar ta Barcelona a watan Oktoba.

A gefe ɗaya, babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid, ita ma ba ta taɓuka komai ba a wannan kakar, inda yanzu haka take matsayi na huɗu a gasar bayan 1-1 da ta yi da Villarreal a ranar Asabar.